Ba da tazarar haihuwa na taimakon lafiyar iyali – Rejoice Bala
Wata jami’ar kula da lafiya a matakin farko a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Gombe mai suna Malama Rejoice Bala, ta ce bayar da tazarar haihuwa yana taimakawa wajen inganta rayuwar iyali. Malama Rejoice Bala wadda ke bangaren kula da ba da tazarar haihuwa a jihar ta ce ba da tazara tsakanin haihuwa na taimaka wa […]

Wata jami’ar kula da lafiya a matakin farko a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Gombe mai suna Malama Rejoice Bala, ta ce bayar da tazarar haihuwa yana taimakawa wajen inganta rayuwar iyali.
Malama Rejoice Bala wadda ke bangaren kula da ba da tazarar haihuwa a jihar ta ce ba da tazara tsakanin haihuwa na taimaka wa uwa musammam wajen kara samar mata lafiyar jiki.
Malama Rejoice Bala, ta bayyana haka ne lokacin da take zantawa da Aminiya a Gombe bayan kammala wani taron ’yan jarida da masu ruwa-da-tsaki da wata kungiya mai suna Mamaye E4A, ta shirya don fadakarwa kan muhimmancin bayar da tazara a tsakanin haihuwa.
Ta ce idan iyalai suna ba da tazara a tsakanin haihuwa yana taimaka wa uwa daga irin jinin da ta zubar ya sa ta samu karfin jiki da samun damar kula da ’ya’ya da kuma maigida.
Malama Rejoice ta ce gwamnati na bakin kokari wajen fadakar da jama’ar karkara don su san muhimmancin ba da tazara haihuwa da kauce wa haihuwar kunika da wadansu mata ke yi da ke haifar musu da matsalar lafiya.
Ta ce suna hada kai da ’yan jarida da malaman addinai da sarakuna don sakon ya isa inda ake so musamman ga mutanen karkara.
Jami’ar ta yi kira ga maza su rika barin matansu suna zuwa awo a asibitoci lokacin da suka samu juna domin samun shawarwarin kwararru kan lafiyarsu.
Ta ce akwai magungunan ba da tazarar haihuwa kyauta a asibitoci amma ba a zuwa a karba saboda har yanzu wadansu ba su san muhimmancin ba da tazarar iyali ba.