Ba da yawuna aka ba Shekarau takarar Kano ta Tsakiya ba —AA Zaura
AA Zaura ya ce an “kwace” masa burin takarar kujerar Kano ta Tsakiya ba tare da yardarsa ba. Ya bayyana cewa ba a gayyace shi taron ba kuma ba a tuntuɓe shi kan shirin siyasar da ya shafi tikitin ba.
Mai neman takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a Jam’iyyar APC, Abdulsalam Abdulkarim Zaura (AA Zaura) ya yi zargin an ƙwace burinsa na yin takara bayan da jam’iyyar ta ba wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, takarar.
Hakan na zuwa ne bayan ’yan takara guda shida da ke neman kujerar Sanata a Kano ta Tsakiya APC janye takararsu tare da mara wa Sanata Shekarau baya, bayan taron sulhu da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shirya.
Taron, wanda aka gudanar a Abuja, ya yi nufin kawo ƙarshen rashin jituwa da ya ɗauki makonni tsakanin jiga-jigan jam’iyyar kan yadda Shekarau ya fito a matsayin ɗan takarar da aka cimma matsaya a kansa kafin zaben 2027.
Sai dai ɗaya daga cikin manyan masu neman takarar a jam’iyyar ta APC, Abdulsalam Abdulkarim Zaura (AA Zaura), bai halarci taron ba.
- Gwamnan Bauchi: Zan kayar da ɗan takarar Gwamna Bala Mohammed — Ɗan takarar PDP
- Kwamitin Amintattu na ACF ya yi watsi da dakatar da shugabansa
A madadin sauran ’yan takarar, Usman Bala ya bayyana cewa sun yanke shawarar janye takararsu domin zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a cikin jam’iyyar.
Ya ce: “Mun janye takararmu da mutunci domin ba wa Sanata Ibrahim Shekarau dama, don tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a APC. Mun amince da matsayar da aka cimma a taron sulhu, kuma muna ba da cikakken goyon bayanmu ga nasarar jam’iyyar.”
’Yan takarar da suka janye sun haɗa da Usman Bala, Sha’aban Sharaɗa, Ɗanyaro Yakasai, Abbas Sani Abbas, Abdulfatah Zango da Shehu Isah Direba.
Majiyoyi daga taron sun ce shiga da Gwamna Abba ya yi, ya taimaka wajen kwantar da hankali tsakanin jiga-jigan jam’iyyar tare da shawo kan ’yan takarar su mara wa Shekarau baya a matsayin ɗan takarar da aka cimma matsaya a kansa.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Abba ya bayyana wannan sulhu a matsayin babban ci-gaba na siyasa ga jihar Kano da jam’iyyar APC.
Sanarwar ta ce Kano ta Tsakiya, wadda ta ƙunshi ƙananan hukumomi 15 da yawan jama’a sama da miliyan 10, na da muhimmanci matuƙa a lissafin siyasar jihar.
Gwamnan ya yaba wa ’yan takarar da suka sadaukar da burinsu domin haɗin kan jam’iyya da daidaituwar dimokuraɗiyya. Ya ce: “Shawarar da suka yanke na nuna dattaku, sadaukarwa da jajircewa wajen ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya.”
Gwamna Abba ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da amfani da tattaunawa, haɗin kai da cimma matsaya a matsayin kayan aiki na kwanciyar hankali da ci gaban siyasa mai ɗorewa.
An ƙwace min burin takara —AA Zaura
A nasa ɓangaren, AA Zaura ya ce an “kwace” masa burin takarar kujerar Kano ta Tsakiya ba tare da yardarsa ba. Ya bayyana cewa ba a gayyace shi taron ba kuma ba a tuntuɓe shi kan shirin siyasar da ya shafi tikitin ba.
Ya ce: “Ba a gayyace ni ba. Ban san da taron ba, kuma babu wanda ya nemi in halarta.”
Da aka tambaye shi kan matsayinsa, ya ce ba zai ci gaba da neman kujerar ba. “Matsayina yanzu shi ne an ƙwace min wannan buri, an sace shi, ba tare da yardata ba.”
Sai dai ya bayyana cewa bai sayi fom ɗin takara ba, saboda tsarin farko shi ne gwamna zai sayi fom ya ba wanda ya zaɓa a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
“Tsarin farko shi ne gwamna ya sayi fom ya ba wanda ya zaɓa. Lokacin da gwamna ya shaida min kada in sayi fom, ban sayi ba.”
Ko da yake bai ambaci Shekarau kai tsaye ba, maganganun Zaura na iya ƙara tayar da muhawara a cikin APC kan yadda aka gudanar da tikitin Kano ta Tsakiya kafin zagayen zaɓe na gaba.
A nasa jawabin a taron sulhu, Shekarau ya yaba wa Gwamna Abba kan yadda ya kawo zaman lafiya tsakanin jiga-jigan jam’iyyar, tare da gode wa ’yan takarar da suka mara masa baya.
Ya kuma yi kira ga ’yan jam’iyya da su ci gaba da zama ɗaya domin nasarar APC a Kano da ma ƙasa baki ɗaya.