Ba dabi’ar malaman Sunnah ba ne su ce wane yana wuta – Sheikh Kabiru Gombe

Babban Sakataren kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe, ya ce ba dabi’ar Ahlus Sunnah ba ne su ba mutum Aljannah ko su ce wane yana wuta, don haka jita-jitar da aka rika yadawa cewa ya ce Fadar Bege yana wuta wani shiri ne kawai na a nema […]

Ba dabi’ar malaman Sunnah ba ne su ce wane yana wuta – Sheikh Kabiru Gombe

Babban Sakataren kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe, ya ce ba dabi’ar Ahlus Sunnah ba ne su ba mutum Aljannah ko su ce wane yana wuta, don haka jita-jitar da aka rika yadawa cewa ya ce Fadar Bege yana wuta wani shiri ne kawai na a nema wa marigayin suna, inda ya ce duk wanda ya kawo kaset din da ya fadi wannan magana zai ba shi Naira miliyan 10.
Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da wa’azi a harabar Masallacin Utako da ke Birnin Tarayya, Abuja a ranar Juma’ar da ta gabata, inda ya ce labaran da aka rika yadawa a wuraren Mauludi da hotunan da aka rika sanyawa a kafar sadarwa ta Facebook cewa Allah Ya canja halittarsa saboda ya ce Fadar Bege yana wuta zance ne da wani malami ya shirya domin ya nema wa Fadar Begen mabiya kuma a karshe ya janye mabiya zuwa gare shi.
Sheikh Kabiru Gombe ya ce, wannan ya nuna ruderwar mabiya dariku,“domin idan za su ce mun matsa wa su Sheikh Tijjani da Sheikh Kaulaha, amma ba su cutar da mu ba, bai dace don mun bata waliyi mai ganga in ma mun bata shin, a ce Allah Ya sauya mana halitta ba, saboda fadar hakan na nuna waliyi mai ganga ya fi wadancan shehunnai ke nan,” inji shi.
Sheikh Kabiru Gombe, ya ce ba haka Allah yake al’amarinSa ba, domin haka ya yi nasiha ga magoya bayan kungiyar Izala su daina nuna damuwa kan ire-iren wadannan maganganu. Ya ce ya ji mamaki da mutane suka rika kiransa ta waya kan wannan shirme da ko hankali ba zai dauke shi ba.
Shi ma da yake gabatar da nasiha Sautus Sunnah Sheikh Yakubu Musa Katsina ya nemi magoya bayan kungiyar su daina damuwa da irin wadannan maganganu inda ya ce a baya an rika buga hoton wani mutum da kan jaki ana cewa na dan Izala ne, amma sai ga shi yau Izala ta shiga gidan kowa.
A nasihar shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce, wannan kazafi maimakon bakanta Izala sai ya kara mata kwarjini, inda ya ce bayan wa’azin da suka gabatar tare da Sheikh Kabiru Gombe a Kano, mutane da dama sun dawo daga rakiyar irin wadancan malamai da suka shara karya don nuna karamar karya.