Ba diyarmu ce ta kai hari a Kamaru ba – Iyayen ‘yan matan Chibok
Wasu daga cikin iyayen ‘yan matan Chibok sun ce yarinyar nan da dakarun kasar Kamaru suka kama tana shirin kai harin kunar bakin-wake ba daya daga cikin ‘ya’yansu ba ce. Iyayen sun bayyana hakan ne bayan da suka duba hotunan yarinyar. Shugaban iyayen ‘yan matan Chibok, Yakubu Nkike, wanda na daya daga cikin wadanda suka […]

Wasu daga cikin iyayen ‘yan matan Chibok sun ce yarinyar nan da dakarun kasar Kamaru suka kama tana shirin kai harin kunar bakin-wake ba daya daga cikin ‘ya’yansu ba ce.
Iyayen sun bayyana hakan ne bayan da suka duba hotunan yarinyar.
Shugaban iyayen ‘yan matan Chibok, Yakubu Nkike, wanda na daya daga cikin wadanda suka duba hotunan, ya ce “yarinyar ba ta yi kama da ‘yan mata na Chibok ba.”