…Ba dole ne masallaci ya yi saiti da Ka’aba ba

Taso da irin wannan zancen zai jawo ringingimu    -Sheikh dahiru Bauchi Fitattacen Malamin nan Shaikh dahiru Usman Bauchi ya janyo hankalin musulmi dangane da zancen matsalar  alkibla na massallatai da cewa su yi hakuri su bar wannan magana, domin taso da irin wannan zance zai janyo rigingimu ne kawai a tsakanin al’umma. Malamin ya bayyana […]

…Ba dole ne masallaci ya yi saiti da Ka’aba ba
…Ba dole ne masallaci ya yi saiti da Ka’aba ba

Taso da irin wannan zancen zai jawo ringingimu    -Sheikh dahiru Bauchi

Fitattacen Malamin nan Shaikh dahiru Usman Bauchi ya janyo hankalin musulmi dangane da zancen matsalar  alkibla na massallatai da cewa su yi hakuri su bar wannan magana, domin taso da irin wannan zance zai janyo rigingimu ne kawai a tsakanin al’umma.
Malamin ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da Aminiya a gidansa da ke  Kaduna.
Shaikh dahiru Bauchi ya ce, idan an samu matsalar alkibla a masallaci sai a gyara domin a cigaba da sallah a cikin  masallacin.
Ya ci gaba da cewa,  Annabi (Sallallahu Alaihim wasallam) a Madina kudu suke duba su yi sallah, domin su suna arewa ne da garin  Makka, ya ce idan mutum ya tsaya ya sa hannunsa daya a mafitar rana, hannunsa daya a mafadar rana, idan ya dubi gabansa ya zama alkibla. “ Saboda haka yadda ake duban gabas a yi sallar nan a cigaba da yin haka, idan wadansu masana sun ce bai yi daidai ba, shi ke nan sai a sake, idan kaucewar  ya yi yawa.Amma idan bai yi yawa ba ai babu komai.’’
Da yake amsa tambaya a kan ta yaya za’a fahimce alkibla bai yi daidai ba? Sai ya ce, “ wadanda suka fada su suka jawo, da ba a fadi ba da sai dai kawai a cigaba da sallah, domin babu yadda za a yi wanda yake cikin Haramin Makka ainihin ginin Ka’aba shi ne kiblarsa idan yana cikin masallaci.  “ Kana kallon ginin shi za ka duba ka yi sallah, idan ka fita daga masallacin kuma shi masallacin za ka duba ka yi sallah idan kana cikin garin Makka, idan ka fita Makka kuma wajen Makkan za ka duba ka yi sallah. Idan ka tafi yamma da Makka, to gabas za ka duba ka yi sallah. Idan kana gabas da Makka Yamma za ka duba ka yi sallah, idan kuma kana arewa da MaKka, kudu za ka duba ka yi sallah. Idan kana kudu da Makka, arewa za ka duba ka yi Sallah.’’
“ Idan kana wani bangare da shi ba kudu ko Arewa ba, sai su nuna maka yadda za ka dan karkata. Amma irin wannan zancen jawo shi zai kawo wata magana mai yawa, domin akwai masallatai da Sahabbai ne suka kafa su a Afirka, a wadansu wurare idan an samu irin wadannan sai a kwatanta  inda su Sahabban suka yi sai a bi nasu.’’
“ Amma taso da irin wadannan maganganu yakan taso da rigingimu masu yawa, domin za a nuna ke nan cewa su mutanen baya da suka yi sallah ke nan ba su yi daidai ba,” inji shi.
Da aka tambaye shi ko wane irin jan hankali zai yi ga al’umma kan wannan zancen sai ya ce, “ idan dai kaucewar bai yi yawa ba sai a yi ta sallah, amma idan masu dubawan suka ce kaucewar ya yi yawa sai a duba a daidaita yadda zai yi daidai. Idan kaucewar dai ba ta yi yawa ba sai a yi ta sallah, domin sanin gaibu sai Allah, inji Hausawa.’’

Gara a gyara barna maimakon ci gaba da tafiya a kanta      -Usman Mahmud

Adam Umar, Abuja

Malam Usman Mahmud yana cikin wadanda suke amfani da na’ura wajen gano alkiblar masallatai a kasar nan da suka gano masallatai da dama ba su fuskantar Ka’aba, Aminiya ta zanta das hi kamar haka:

Aminiya: Sai ka gabatar mana da kanka
Usman Mahmud: Sunana Usman Mahmud, ni jam’i ne a sashin nazari kan ganin wata da kuma fayyace alkibla (moon sighting and kibla determination) a Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci na Najeriya.
Aminiya: Me ya ba ku kwarin gwiwa wajen nazari a kan masallatai har kuka gano wadansu daga cikinsu ba sa kan hakikanin alkibla?
 Usman Mahmud: A sakamakon korafi da ake ta yi na rashin hadin kai a tsakanin al’ummar musulmi, ni da abokan aikina mun yi nazarce nazarce, sai muka kula akwai masallatai da dama da ba sa fuskantar hakikanin alkibla. wadansu na fuskantar wurare irin su Madagaska ko Habasha ko Isra’ila. Mun kyautata zaton cewa watakila da za mu inganta fuskantar da masallatanmu a kan alkibla kamar yadda muke kyautata sahu a yayin Sallah, watakila za a samu nasara wajen samun hadin kan musulmai.
Sai dai abinciken da muka yi, wanda muna yi ne ta hanya nazari da manhajar  kwamfuta da ya shafi na Google earth, da Satellite image, da GPS, mun gano cewa yawancin masallatai da aka gina a da can ko wadanda aka maida tubalinsu a kansu, suna kan ka’ida, saboda a lokacin da aka gina su an bi ka’idoji na shari’a da kuma nazari ta hanyar  taurari da rana da dutsi, da dai sauransu, wanda Shehu Usman dan Fodiyo da ma Almajiransa daga bisani suka jajirce wajen tabbatar da hakan. Sabanin yawancin masallatan da aka gina daga baya-bayan nan, inda aka bi fatawar daidaikun daliban ilimi.
Aminiya: A nazarin da kuka yi, kamar wadanne masallatai ne kuka gano ba sa kan hakikanin alkibla?
Usman Mahmud: Masallatan na da yawa, sai dai idan za mu yi bayanin muhimmai a cikinsu, akwai babban masallacin kasa na Abuja da na Sultan Bello da ke Kaduna da na fadar Sarkin Kano da na Isiyaka Rabi’u  da na kofar Mata, duk a Kano, da wani Masallaci da Bafarwa ya gina mai suna Maccido Islamic center, da babban Masallacin Jos (Nasrul Islam) da na fadan sarkin Gombe, da na garin Gindiri a jihar Filato, da na Sarkin Ofa, da babban masallacin Katsina, da dai masallatai da dama. Sai dai akwai wadanda Alkiblarsu ke kan tsari, kamar yadda na gaya maka a baya, kuma masallatan sun hada da babban Masallacin Juma’a na kasa na farko da ke Area one a Abuja, da na Usman bin Affan da ke Baned plaza, sai kuma na Idi na kofar mata Kano, da babban Masallacin garin Daura, sai kuma daukacin masallatan barikokin Soja da ke nan Abuja, wadanda muka gano cewa ya faru ne a dalilin tsarin da ake bi wajen gina barikoki ta hanyar amfani da gabas da yamma (cardinal point), kamar dai yadda aka gina mafi yawan unguwanni GRA na kasar nan a baya.
Wadansu masallatan kuma a farko ba sa kan hakikani Alkibla, amma aka gayyacemu muka nuna musu hakikanin Alkibla suka gyara, wadansu kuma aka sake ginin gaba daya, idan sun tashi fadada masallacin, kamar dai na Baned Plaza, wadansu kuma an gyara su ne daga shimfidarsu, kamar na Izala da ke Bega junntion, duk dai a nan Abuja. Wadansun kuma mukan fitar musu ne kafin fara aiki ko bayan sun fara, kamar na Mopol Barrack Deidei, da na Lugbe Abuja. Sai kuma na Salamatu Institute Tudun Wada Kaduna, da na Algarkawi, da na Kinkinau, duk a Kaduna, da dai sauransu.
Misali da na yi da fitar da Alkiblar Masallaci ta hanyar amfani da dutse kuma, wannan ya faru ne tun a zamanin Manzon Allah (SAW) a lokacin da ya aika wani sahabi zuwa kasar Yaman ya yi wa wadansu al’umma da’awa, sannan ya ce idan sun musulunta ya jagoranci gina musu masallaci da zai fuskanci wani dutsi mai suna jabaluddin, wanda hakan ke nuna cewa wahayi aka yi wa Manzon Allah (SAW) ya fahimci cewa alkiblan garin na fuskantar dutsen ne, kasancewar a lokacin bai taba zuwa garin ba.
Wani malami mai suna Sheikh Abdulmajid Albengani ya yi wani bayani (Documentary) mai tsawon minti goma da ya yi amfani da tsarin Google earth wajen nazari a kan taswiran dutsen da dakin Ka’aba, inda ya gano cewa waje guda suke fuskanta, ya ayyana cewa tsarin Google earth ya tabbatar da mu’ujiza da Annabcin Manzon Allah (SAW), kasancewar a lokacin da ya bada umarnin bai taba zuwa kasar da dutsin yake ba.
 To a yanzu haka idan ka auna wani dutei ka ga taswirarsa ya daidaita da Ka’aba  kana iya sanar da jama’a su rika fuskantar da masallatansu ta wajen. Kamar yadda a bangaren taurari kuma ake kwatance da wadansu taurari da  ake yi wa lakabi da kaza mai ’ya’ya, wadanda yawanci mutanen karkara a kasar Hausa sun san da su. Sai dai kash! a yanzu sau da dama sai ka ga Alkiblan Masallatai da dama na hannun riga da wadannan taurarin.
Aminiya: Ta yaya kuke gano masallaci daga sauran gine-gine a taswirar Goagle earth da kuke amfani da shi a manhajar Kwamfutar?
Usman Mahmud: Da farko idan ka zakulo taswirar gari  za ka gane masallaci ne da husumiya, ko bishiyoyi a wani zubin, da ke kewaye da shi, ko kuma wajen tsayuwar liman, idan karami ne, sannan ka tabbatar da hakan idan ka jawo shi. Za ka kuma gane masallacin na waje kaza ne ta hanyar kula da tituna ko wadansu alamu da ka san wajen ne kadai ke da su a garin. Sai mu auna kibiya a kan masallacin tare da jan kibiyar zuwa dakin ka’aba a taswiran duniya na Goole earth, mu ga ko sun daidaita a Alkibla ko kuma akwai karkata.
Aminiya: Amma a kwanakin baya Majalisasr koli ta addinin Musulunci ta shiya zama a nan Abuja a kan wannan al’amari, inda a karshen zaman kuka cimma matsaya cewa karamin karkacewa irin na Masallacin Abuja ga misali, bai saba alkibla ba, matukar ba ya yi muni ba ne.
Usman Mahmud: Shisshigi aka samu a lokacin daga wadanda ba ma’abota al’amari ba, ko masana, har wani ya yi misali da wani masallaci a Amurka da wadansu ’yan uwa ke amfani da wani gini da suka samu a matsayin masallaci. Wanda a lokacin ganin su sabbin musulunta ne ga kuma al’amarin mahalli a wajen, aka ba su fatawa na su karkatar da shimfidar wajen a maimakon rusa shi. Kuma a lokacin mun dai yi shiru ne ba don gamsuwa da bayanai da hanzarin da wadansu malamai suka bayar ba, mun da hakura ne kawai saboda gudun wadansu abububuwa, ba don mun gamsu  da bayanansu ba.
Aminiya: To wane kira ka ke da shi a kan hakan:
 Usman Mahmud: Ina kira ga malamai da su guji bada fatawar cewa duk inda aka duba a bangaren gabas Alkibla ne. Saboda mai Fikihus Sunnah ya taka wa masu dogaro da wannan hadisi birki, inda ya nuna cewa hadisin na bayani ne a kan mutane garin Madinah kadai, ya yi misalin cewa Alkiblar mutanen Misira daban take da ta Madina, haka ta mutanen Indiya wadanda Alkiblarsu Yamma ce. Kamar yadda mu kuma a nan Najeriya da ke yamma maso Kudu da Makka, Akiblarmu ita ce Gabas maso Yamma.  Ina kuma tunatar da su cewa kakanninsu irin su Shehu Usman dan Fodiyo ba haka suka bi ba, sun yi amfani da tsarin taurari da sauran alamu irinsu rana ne. Kuma su san da cewa idan matasa da ke tasowa a yanzu wadanda suke karanta ilimin addini da na kimiyya a lokaci guda, idan suka gano wadannan matsaloli a nan gaba, to ba za su gansu da kima ba. Kuma a karfafa gyara barna idan aka gano ta a maimakon cigaba da tafiya a kanta da sunan gudun magana.
Aminiya: Me ya sa kuka watsar da tsarin amafani da alamu irin su Rana da wata, kuka rungumi amfani da na na’urar zamani?
Usman Mahmud: Hada su muke yi waje guda mu yi amfani da su. Kamar rana muna amfani da ita wajen nazari a kan ta inda take fitowa, sannan kuma da lokutan da  take sauya wajen fita, sai kuma tsayuwar inuwa.