Ba dole ne masallaci ya yi saiti da Ka’aba ba -Malamai
An dade ana ta maganganu dangane da inda masallatan kasar nan suke fuskanta, inda wadansu masana suka nace a kan cewa masallatai da dama ba su fuskantar Ka’aba, hasali ma dai wadansu suna fuskantar wadansu kasashe ne dabam. Aminiya ta tuntubi malamai domin jin yadda za su warware matsalar.Duk wanda ya kalli gabas ya yi […]
An dade ana ta maganganu dangane da inda masallatan kasar nan suke fuskanta, inda wadansu masana suka nace a kan cewa masallatai da dama ba su fuskantar Ka’aba, hasali ma dai wadansu suna fuskantar wadansu kasashe ne dabam. Aminiya ta tuntubi malamai domin jin yadda za su warware matsalar.Duk wanda ya kalli gabas ya yi daidai -Sheikh Jingir
Wakilinmu Hussaini Isah ya tattauna da Shugaban Majalisar malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir kan wannan lamarin. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya. Mene ne Malam zai ce dangane da amfani da na’urar nan wadda take gwada yadda alkibla take a masallatan kasar nan?
Sheikh Jingir. To, da farko dai Sallah daya ce daga cikin rukunan addinin musulunci guda biyar. Kuma addinin musulunci addini ne na Allah wanda Ya halacci duniya da lahira domin mu bauta masa da addininsa na musulunci. Abu na biyu, Allah bai yarda mutum ya yi addinin nan da ka ko da ra’ayi ba. Ya zabi Annabawa manzanni ya aiko su da sakon addini, ya kawo shugabansu Annabi Muhammad (SAW) wanda yake shi ne na karshe. Kuma Allah Ya aiko Annabi Muhammad (SAW) da littafin Alkur’ani mai girma wanda barna ba ta zuwa gabansa da bayansa. Kuma sai da aka kammala addini kaf sannan Annabi Muhammad (SAW) ya bar duniya, ba a bar wani gurbi da wani zai zo ba. Kuma Sallah ita ce ta biyu a cikin rukunan musulunci, kuma fuskantar Alkibla yana daya daga cikin sharudan Sallah.
An haifi Annabi Muhammad (SAW) a garin Makka, bayan ya shekara 40, Allah Ya yi masa wahayi na addinin musulunci. A lokacin idan zai yi Sallah yana fuskantar dakin Allah ne, wato Ka’aba, domin nan ne Alkiblar da Annabi Ibrahim (AS) ya fuskanta lokacin da Allah Ya aiko shi duniya.
A lokacin sai Allah Ya umarci Annabi Muhammad (SAW) ya yi kaura daga garin Makka zuwa garin Madina. Da ya koma Madina bayan ya yi shekaru 13 a garin Makka da samun wahayi, sai Allah Ya ba shi umarnin ya fuskanci Alkiblar Baitul Mukadis da ke Falastin idan zai yi Sallah. Don haka a lokacin idan zai yi Sallah yana fuskantar Baitul Mukadis ne.
A lokacin da Yahudawa suka ga Annabi Muhammad (SAW) yana fuskatar masallacin Baitul Mukadis, idan zai yi Sallah. Sai suka rika yin soke-soke da gori, suna cewa ga shi nan ya ki bin addinin da suke bi na Yahudanci da addinin Nasaranci, amma yana fuskantar Alkiblar da suke fuskanta. Wannan abu ya zamanto yana damun Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW).
To ba dama ya yi wani abu sai abin da Allah Ya umarce shi ya yi. Sai ya rika daga kai sama yana rokon Allah Ya mayar da shi ga Alkibla ta Annabi Ibrahim( AS) saboda wannan gori da Yahudawa suke yi masa. Sai Allah a cikin Alkur’ani mai girma ya ce masa tabbas ina ganin jujjuyawar fuskarka a sama don neman a yi maka wahayi kan hukumcin Alkibla. Allah Ya ce da sannu za mu fuskantar da kai ga Alkiblar da kake yarda da ita. Daga baya sai Allah Ya ce ka fuskatar da fuskarka idan za ka yi Sallah zuwa ga jihar da masallaci mai alfarma yake, wato Ka’aba ke nan.
Ka ga Allah Ya dauke shi daga fuskantar masallacin Baitul Mukadis Ya mayar da shi zuwa ga fuskantar Ka’aba. Sai Allah Ya ce a duk inda al’ummar musulmi kuke ku juyar da fuskarku zuwa ga jihar da Ka’abi take. Lalallai wadanda aka ba su littafi Yahudawa da Nasara su da kansu da suka karanta Attaura da Injila, wallahi suna sani cewa yadda ka fuskaci Alkiblar nan ta Ka’aba gaskiya ne. Don yana nan a cikin Attaura da Injila cewa Annabin karshen zamani da Allah zai aiko zuwa ga duniya gabaki daya idan ya zo zai kalli Alkiblar masallacin Baitul Mukadis kuma zai juya zuwa ga Ka’aba.
Allah ya ce, amma suna gaba da musulunci suna kokarin su batar da mutane daga ainihin inda Alkibla take. Sai Allah Ya ce bai rabkana da abin da Yahudawa suke yi ba.
Don haka idan muka dubi wannan magana ta wannan na’ura wadda ake amfani da ita wajen duba Alkibla a masallatanmu za mu ga ba ta da asali. Domin farko idan muka duba za mu ga cewa Annabi Muhammad (SAW) ne aka fara aikowa da Sallah don ya sanar da duniya. Kuma Allah Ya umarce shi ya fuskanci Baitul Mukadis idan zai yi Sallar, sai da ya yi watanni 16 zuwa watanni 17 yana fuskantar Baitul Mukadis, sannan Allah Ya canza masa Ya ce ya fuskanci Ka’aba wadda dama ita yake fuskanta ya yi Sallah kafin ya yi hijira zuwa garin Madina.
Sai Allah ya ce a duk inda kuke ya al’ummar musulmi ku fuskanci jihar da masallaci mai alfarma yake. Shi yasa mu da muke yamma da masallaci mai alfarma na Ka’aba, wato mutanen Afrika ta yamma. Idan muka tashi yin Sallah muke fuskantar jihar da masallaci mai alfarma Ka’aba yake. Wato mu kalli gabas fakaka. Wadanda kuma suke gabas da Makka su ma sai su dubi jihar da masallaci mai alfarma na Ka’aba yake fakaka, wato su fuskanci yamma. Haka kuma wadanda suke kudu sai su fuskanci arewa da fadinta don su kalli Alkibla. Wadanda kuma suke arewa sai su fuskaci jihar kudu. Wato kowace kusurwa mutum yake zai kalli jihar da masallaci mai alfarma na Ka’aba yake.
Sai ya zamanto hukumcin fuskatar Alkibla ga wanda yake kwaryar masallacin mai alfarma gashi ga Ka’aba yana ganin a, to shi sai ya yi saiti sak. Amma ga wanda yake waje, shi idan ya tashi yin Sallah sai ya fuskanci jihar da Ka’abar take.
Kuma mu musulunci ya shigo Nijeriya ne fiye da shekaru 1000 da suka gabata. A yau kuma sai ga wani ya zo da wata na’aura wai zai gwada ya ga masallatanmu suna kan Alkibla ko ba sa kan Alkibla. Alhalin an yi sama da shekaru 1000 da kafa umarnin Allah da koyarwar Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW) kan idan za mu yi Sallah mu fuskanci jihar da dakin Ka’aba yake. Kuma mu a wajenmu jihar da dakin Ka’aba yake shi ne gabas. Babu wanda ya wajabta mana cewa sai mun yi saitin dakin Ka’aba kamar za mu je mu taba shi da hanunmu.
To, kuma ita wannan na’ura da aka kawo, mene ne za ta gaya mana kan sallolin al’ummar musulmanmu na sama da shekaru 1000. Kuma wane ne ya kera wannan na’ura? musulmi ne ko kafiri? Yahudawa dangane da maganar Alkibla sun yi ta zage-zage da gori ga Manzon Allah (SAW) da sukar addinin musulunci tun a wancan lokaci. To, daga gare su ne kuma yanzu za mu samu sabuwar Alkibla don su karkatar da musulmi. Kuma sune aka ce su koya mana, bayan ga Alkur’ani mai girma a hanunmu ya ce mu fuskanci jihar da Ka’aba take idan za mu yi Sallah?
Don haka maganar wannan na’ura ba magana ba ce. Ina tsammanin fadan nan ne na Yahudawa tun na farkon lokacin nan da suka rika cewa wai Annabi Muhammad (SAW) yana kallon Alkiblarsu ta Baitul Mukadis bayan ya ki addinin su, da Allah kuma Ya canza masa har yanzu suna nan da wannan gabar Suke neman su batar da wanda bai yi karatu ba.
Don haka wannan maganar ta’ura ba gaskiya ba ne. Abin da Alkur’ani ya fada kan maganar Alkibla shi ne mu fuskanci jihar da Ka’aba take fakaka. Don haka dukkan masallatanmu masu kallon jihar da Ka’aba take a Makka suna nan daidai bisa ga ayar Allah da koyarwar Manzon Allah Annabi Muuhammad (SAW). Wanda har ya bar duniya babu wannan na’ura. Sahabai sun yi rayuwarsu sun wuce babu wannan na’ura, tabi’ai sun yi rayuwarsu sun wuce babu wannan na’ura. Don haka wannan na’ura mai yuwuwa ne an turo su ne don su jefa wa musulmi shakka, kuma da yardar Allah ba za su iya ba. Domin Alkur’ani mai girma yana nan, koyarwar Manzon Allah (SAW) tana nan, babu wanda aka dora wa cewa idan zai yi Sallah sai ya yi wani dogon nazari na kimiyya tukuna. Don haka dukkan masallatan da suke Nijeriya da Ghana da Masar da dukkan masallatan da aka gina, matukar sun dubi gabas sun yi daidai. Babu wanda ya ce sai an kawo wata na’urar da babu ita tun da.
Aminiya. Wato a takaice dai shari’a ba ta amince a yi amfani da wannan na’ura wajen duba Alkibla ba a masallatai ba?
Sheikh Jingir. Ita wannan na’ura ba ita ce tushen duba Alkibla ba. A fuskanci jihar da Alkibla take kawai sai a yi Sallah. Idan kuma mutum ya je ya shiga wata ruguguwa, ko a daji, ko ya je wani gari ya kasa sanin inda yake. Shi ke nan idan yana da wannan na’ura sai yi amfani da ita ya duba inda gabas take. Idan haka ta kasance mutum ya yi amfani da wannan na’ura babu wanda zai ce ya yi laifi. Amma wannan na’ura ba ita ce tushe ba.
Aminiya. Shin Malam dole ne sai masallaci ya kalli Alkibla zai yi Sallah ?
Sheikh Jingir. Dole ne sai masallaci ya fuskanci Ka’aba, domin Ka’abar Allah Ya riga Ya fadi yadda za a yi a fuskance shi, domin ba zaka iya kallonsa da idanunka a gabanka ba. Amma idan kana cikin masallacin dole sai ka yi saitin Ka’abar, amma idan kana nesa da masallacin Ka’abar sai ka nemi jihar da Ka’abar take ka fuskanta kayi Sallarka. Babu wanda ya ce dole sai ka yi amfani da wata na’ura. Wannan neman yawo da hankalin al’ummar musulmi ne, wanda ba daidai ba ne.
Aminiya. Ina matsayin mutumin da ya yi Sallah a masallacin da ba ya fuskantar Alkibla?
Sheikh Jingir. Wanda ya yi Sallah a masallacin da ba ya fuskantar Alkibla, wato kamar mu a nan Nijeriya mutum ya gina masallaci ya kalli yamma a maimakon ya kalli gabas, to wanda ya yi Sallah a wannan masallaci Sallarsa ba ta yi ba. Amma in dai masallaci yana fuskantar gabas a Nijeriya ko kuma a Afrika idan mutum ya yi Sallah a wannan masallaci ya yi daidai.
Aminiya. To, a karshe wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar musulmi dangane da wannan al’amari?
Sheikh Jingir. Kiran da nake da shi ga al’ummar musulmi dangane da wannan al’amari shi ne, mu sani cewa ba a addinin musulunci da kame-kame ko kuma farfaganda. Ana yin addinin musulunci ne da Alkur’ani da Hadisi da littafan fikihun musulunci. Don haka duk mai neman maganar Alkibla ya dubi Alkur’ani mai girma ya dubi suratul Bakara aya ta 142 zai ga maganar Alkibla baki daya.Sannan ya duba hadisan Manzon Allah (SAW) da suke sharhin wadannan ayoyi.
Kuma ina kira ga al’ummar musulmi kan a karanta Alkur’ani mai girma, a karanta hadisan Manzon Allah (SAW). Idan muka yi haka Allah zai tserar da mu daga dukkan masu kokarin zame mana kafa daga kan tsantsan addinin musulunci.
Cigaba a shafi na 2