Ba dole sai na zama shugaban Nijeriya ba — Peter Obi

Obi ya ce yana so Nijeriya ta kasance ƙarƙashin shugabanci nagari da kowa zai yi alfahari.

Ba dole sai na zama shugaban Nijeriya ba — Peter Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya a ƙarƙashin jam’iyyar Labour a Zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce ba dole ba ne sai ya zama shugaban ƙasar nan ba.

Sai dai Peter Obi ya ce yana so ya ga ƙasar tana aiki yadda ya kamata a ƙarƙashin jagoranci nagari.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito Obi yana bayyana haka ne lokacin bikin murnar cika shekara biyu kan mulki na Gwamnan Abia, Alex Otti.

Ya ce ya kamata a samu shugabanni waɗanda mutane za su yi alfahari da su.

Ya ƙara da cewa haƙƙin shugaba ne ya kare muradun waɗanda yake mulka.

Tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya zo na uku a zaɓen shugaban ƙasar da ya gabata, inda ya sha kaye hannun shugaba Bola Tinubu na jam’yyar APC.