Ba don amfanin kaina na koma PDP ba – Nuhu Ribadu
Kwana uku bayan ficewarsa daga Jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar PDP ta fito fili, tsohon Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) Malam Nuhu Ribadu ya bayyana dalilan da suka sanya shi komawa cikin jam’iyya mai mulki.A cikin wata sanarwa da aka sanya a shafinsa na Facebook, Malam Nuhu Ribadu ya ce, […]
Kwana uku bayan ficewarsa daga Jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar PDP ta fito fili, tsohon Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) Malam Nuhu Ribadu ya bayyana dalilan da suka sanya shi komawa cikin jam’iyya mai mulki.
A cikin wata sanarwa da aka sanya a shafinsa na Facebook, Malam Nuhu Ribadu ya ce, “A tsanake ya dauki wannan mataki” na komawa wata jam’iyya kuma ya yi “haka ne don kokarin tabbatar da wani alheri ba domin wata bukata ta son zuciya ba.”
Sai dai bai yi karin bayani kan wannan alheri da yake nufi ba, amma ya ce nan gaba kadan zai bayyana mataki nag aba da zai dauka a gwagwarmayar siyasarsa.
“Na san abu ne mawuyaci ku fahimci dalilin komawata wata jam’iyya. Amma ina tabbatar muku mataki ne da aka tsaya sosai aka nazarta, kuma ba na fatan in bata wa wani. Kuma ba zan yi wani abu da zai kawo gaba a tsakanina da abokaina koda daga wace jam’iyya ko addini ko yanki ko kabila suka fito.”
Ya kara da cewa:
“Zan fadi mataki na gaba game da gwagwarmayar siyasata nan ba da jimawa ba. Amma a yanzu ina tabbatar muku cewa komawata jam’iyya (PDP) wani yunkuri ne na tabbatar da alheri, ba don son rai ba kamar yadda wasu suke fada. Na gode kan yadda kuka nuna hakuri da ni kan wannan mataki, kuma ga waanda suke goyon bayan gwagwarmayata kuma suke ci gaba da amincewa da ni, ina mika musu cikakkiyar godiya. Kuma ba zan ku kunya ba a wannan sabuwar tafiya.”
Tsohon Shugaban na EFCC wanda ke mayar da martani kan wani rahoto da ya ruwaito shi yana sukar tsofaffin abokansa a APC, ya ce duk da ya bar jam’iyyar adawa, zai ci gaba da daukar shugabanninta da daraja.
Ya ce: “Bari in fadi kowa ya sani, ban bayar da wata sanarwa ina sukar APC ko ’ya’yanta ba, ciki har da Gwamna Kwankwaso da takwaransa Amaechi… wadannan karairayi ne a fili da masu muguwar manufa suka kirkiro don tabar da jama’a da nuna akwai wata jikakkiya a tsakanina da abokaina nagari.”
“Bai kamata a dauki canja jam’iyyata a matsayin wata niyya ta kawo gaba a tsakanina da abokaina da ke cikin wata jam’iyya. Har yanzu ina daukarsu da cikakken mutunci, kuma koda akwai wasu bambance-bambance, na yi imani akwai tsari da hanyar mutunci na warware su. Don haka don Allah a yi watsi da kowane bayani da aka ce ni na yi domin bata sunan wani dan siyasa ban canja jam’iyyata. Ba zan bari a jefa ni a cikin irin wannan rashin mutunci ba,” inji shi.
A ranar Asabar ce Malam Nuhu Ribadu ya koma Jam’iyyar PDP a mazabarsa da Bako da ke karamar Hukumar Yola ta Kudu inda aka ba shi katin zama dan Jam’iyyar PDP mai lamba 1933795.
A ranar Litinin wani mukarrabinsa Hamidu Mahmud da ya jagorancin sayo masa fom din nuna sha’awa da tsayawa takarar Gwamnan Jihar Adamawa a karkashin PDP a zaben Gwamnan Jihar da za a gudanar ranar 11 ga Oktoba, ya ce Ribadu bai shiga PDP don a bas hi tikitin takara kai-tsaye kamar yadda wasu ke fada ba.
Ya ce Ribadu ya rubuta takardar neman a sahale masa don tsayawa takarar kamar yadda ke kunshe cikin tsarin mulkin jam’iyyar don ba shi damar shiga zaben, kuma ya yi fatali da rade-radin da ake yayatawa cewa Shugaba Jonathan ne ya tsaya wa Ribadu don tsayawa takarar.