‘Ba don Boko Haram ba da na samu sakamako mafi kyau a jami’a’
Za mu so ka gabatar da kanka?Sunana Enoch Yohanna. Ni ne Sakataren Sansanin ’Yan Gudun Hijira da ke Sabuwar Kuchigoro a Abuja. Ni dan asalin kauyen Goshen ne da ke karamar Hukumar Gwoza a Jihar Borno. Ina yin hidimar kasa ne a nan sansanin a karkashin wata kungiya mai yada ilimi mai suna Global Integrated […]
Za mu so ka gabatar da kanka?
Sunana Enoch Yohanna. Ni ne Sakataren Sansanin ’Yan Gudun Hijira da ke Sabuwar Kuchigoro a Abuja. Ni dan asalin kauyen Goshen ne da ke karamar Hukumar Gwoza a Jihar Borno. Ina yin hidimar kasa ne a nan sansanin a karkashin wata kungiya mai yada ilimi mai suna Global Integrated Education and boluntary Association. Su ne suka turo ni in rika koyar da yara da ke sansanin. Na kammala karatuna a fanin lissafi da kididdiga a Jami’ar Maiduguri.
Ta yaya batun rikicin Boko Haram ya shafe ka?
Gaskiya zan iya cewa ina daya daga cikin wadanda rikicin Boko Haram ya fi shafa, domin ba na mantawa a ranar 29 ga watan Satumban shekarar 2014 ’yan Boko Haram suka kashe mahaifina da daukacin ’yan uwansa a lokacin da suka kai hari kauyenmu Goshen. A wannan lokacin ina rubuta jarrabawata ta karshe kuma ina kokarin kare binciken da na yi na digiri dina. Kodayake batun Boko Haram bai hana in kammala karatuna ba, amma ya hana ni samun sakamakon da nake buri. Domin da jibin goshi na samu sakamako mai daraja ta biyu, maimakon sakamako mai daraja ta daya da nake sa rai.
Me kake burin ka zama nan gaba?
Ina burin in zama mai koya wa mutane sana’o’in hannu. Ina da sha’awar karfafa mutane da taimaka musu su samu abin dogaro da kai. Na lura cewa idan kana da sana’ar hannu za ka taimaka wa jama’a. Za ka zama mai dogaro da kanka. Ba za ka dogara da gwamnati ta sama maka aikin yi ba. Ita sana’ar hannu za ta rage dogaro ga gwamnati kuma za ta sanya matasa su tallafa wa al’umma kuma su bunkasa tattalin arziki. Kuma na lura sana’ar hannu za ta rage zaman kashe wando da bangar siyasa.
Wane kalubale ka fuskanta lokacin da kake karatu a Jami’ar Maiduguri?
Na fuskanci kalubale da yawa. Da jibin goshi na rika biyan kudin makaranta da sayen littattafan karatu da sauran kayan karatu. Saboda ba ni da wanda zai tallafa mini. Domin a lokacin an kashe mahaifina, saura kiris in ajiye karatu saboda rashin wanda zai dauki nauyina. Na kasance cikin dimuwa da gigicewa da rashin tabbas, na shiga fargaba da tsoro. Kowane lokaci sai na rika tunani mai zurfi da kasancewa cikin rashin kwarin gwiwa. Har ta kai ban san wane mataki zan dauka ba. A lokacin ina ajin karshe, ina yin bincikena na karshe kuma ina fuskantar jarrawabata ta karshe, sai komai ya dagule mini. Na sha wahala sosai, babu isasshen abinci, ba kudi saboda haka sai na kasa samun natsuwa. Zan iya tunawa akwai lokacin da na so zuwa kauye amma babu hanyar da zan bi in je garinmu. Kowace hanya da take da alaka da kauyenmu a rufe take.
Shin ka samu zuwa kauyen naku a lokacin?
Eh! Na je kauyenmu amma fa dole sai da na bi ta kasar Kamaru. Tafiya ce mai nisa saboda zagaye ne kuma galibi tafiyar kasa ce. Bayan na shafe kwanaki ina tafiya cikin ikon Allah sai na iso daidai iyakar Najeriya da Kamaru. Sai suka ce sai na yi rajistar sunana. Haka na bi dogon layi, ga kishirwa, ga yunwa ga gajiya. Mun sha wahala sosai ni da sauran ’yan gudun hijirar da na tarar a wurin. Haka na yi ta bin layi har aka zo kaina aka tantance ni. A lokacin da na iso kauyenmu sai na tarar garin babu kowa ya zama kufai. An kashe mahaifina da ’yan uwansa. Sai na samu labarin cewa mahaifiyata da sauran kannena sun gudu zuwa garin Maiduguri. Daga bisani suka dawo Jihar Nasarawa daga nan kuma sai Abuja. Cikin wannan hali na karasa karatuna na jami’a inda na kammala da sakamako mai daraja ta biyu da maki uku da digo uku. Shi ya sa na ce lamarin Boko Haram ya shafi karatuna. Ba zan taba mantawa da shi ba har abada.
Me ya sa ka yanke shawarar zama a sansanin ’yan gudun hijira?
Na zabi zama a nan saboda ina so in taimaka wa mutanena su samu ilimi kuma su koyi sana’a. Shi ya sa na zama sakatarensu kuma mai magana da yawunsu. Ina lura da su, duk wanda ba ya da lafiya ni nake kai shi asibiti. Muna fuskantar kalubale da yawa a wannan sansani. Saboda haka muna bukatar gwamnati ta taimaka mana da abinci da kayan more rayuwa.