Ba don kudi muke ba da sarauta ba -Sarkin Agege

Sarkin Hausawan Agege da ke Jihar Legas, Alhaji Muhammadu Musa Dogon Kadai ya ce masarautarsa ba ta karbar kudi daga mutane ba ce don ta nada su mukamin sarautar gargajiya a yankin.Alhaji Musa ya yi furucin haka ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya jim kadan bayan nadin da ya yi wa Alhaji Ibrahim Tafida […]

Ba don kudi muke ba da sarauta ba -Sarkin Agege
Ba don kudi muke ba da sarauta ba -Sarkin Agege

Sarkin Hausawan Agege da ke Jihar Legas, Alhaji Muhammadu Musa Dogon Kadai ya ce masarautarsa ba ta karbar kudi daga mutane ba ce don ta nada su mukamin sarautar gargajiya a yankin.
Alhaji Musa ya yi furucin haka ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya jim kadan bayan nadin da ya yi wa Alhaji Ibrahim Tafida a matsayin Mai Samarin Agege, a karshen makon da ya gabata a fadarsa.
Ya ce, “Idan mutum ya cancanci mu ba shi sarauta, muna ba shi ne ba tare da karbar kudi daga wurinsa ba. Muna yin lamarinmu ne a kan tsari da kallon kyakkyawar mu’amalar da ke gudana tsakanin jama’a. Muna duba cancanta ne ba abin duniya ba. Kuma, Alhamdulillahi nade-naden da muka yi, mun yi su ne a cikin walwala da soyayya da kuma fatar alheri a tsakani. A gargajiyance abin da muka gani ana yi shi ne, ana yin kyauta ne ga masarauta, kuma idan ma har mutum yana neman sarauta, kuma ya aika wa fada bukatarsa, ita fada takan duba halayensa ne da cancantarsa, sannan ta ba shi mukamin. Muddin shugabanni suka yi nadi bisa tsoron Allah da adalci, to Allah zai taimake su”.
Ya nemi masu mukaman sarautar gargajiya su ji tsoron Allah su yi adalci a tsakanin al’ummarsu.
Sarkin ya yaba da sababbin masarautun da wasu sarakunan gargajiya na ’yan Arewa da ke kudanci suke nadawa. “Muna marhabin da yadda wasu masarautu ke nada mukamai. Ka ga kamar Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Mai Yasin matsayin uba yake a gare mu. Saboda haka muna maraba da nadin da ya yi”. Inji shi.
Sabon Mai Samarin Agege, Alhaji Ibrahim Tafida ya yi na’am ne sarkin da ’yan majalisarsa kan mukamin da aka nada shi, tare da yi musu alkawarin sauke nauyin da suka dora masa, ba tare da nuna bambanci da wariya ba.
Ya nemi hadin kan dukkan samarin Agege su taya shi da addu’ar Allah Ya yi masa jagoranci a tafiyar da shugabancinsa.