Ba don mu ba da wasu kasashen Afirka sun rushe — Faransa
Ba za a tabbatar da muhimmancin Faransa ba sai ta janye dakarunta a irin wannan kasashen.
Shugaba Emmanuel Macron ya ce da ba don kokarin da sojin Faransa ke yi ba, da yanzu wasu kasashen Afirka sun rushe.
Macron ya yi wannan batu ne yayin da yake sake jadadda muhimmancin da kasar ke da shi ga tsaron yankin Sahel.
- Za mu dauki fansar dakarun da aka kashe a Neja — Rundunar Soji
- Mun kakkabo jirage marasa matuka 42 daga Ukraine —Rasha
Wannan na zuwa ne bayan da kasashe rainon Faransa musamman na yankin Sahel ke ci gaba da kufcewa daga hannun ’yan dimokuradiyya, yayin da adawa da kasancewar Faransa a wadannan kasashe ke kara kamari.
A wata tattaunawa da manema labarai, Shugaba Macron ya ce ba za a tabbatar da irin kokarin da sojojinsa ke yi a irin wadannan kasashe ba, har sai an hango yadda za su kasance idan babu sanya hannun Faransa a tabbatar da tsaron.
A shekarar da ta gabata, Faransa ta kara yawan sojojinta da ke rundunar Barkhane mai yaki da ta’addanci zuwa dubu 5,100, sai dai kuma jama’a da gwamnatin sojin wadannan kasashe na korafin cewa, hakan ba shi da wani tasiri.
Shugaba Macron ya kuma bigi kirjin cewa, nasarar da suka samu ta fannin tsaro a kasashen ta zarta wadda wasu kasashen duniya da Kungiyar Tarayyar Turai suka samu idan an hada waje guda, yana mai cewa nan ba da jimawa za su sake sabon salon tunkarar ‘yan ta’addar a irin wadannan kasashe.