Ba don siyasa nake ayyukan raya addini ba – Chakis

Alhaji Shitu Ahmed wanda aka fi sani da Chakis dan gidan sarauta ne a Lafiya Jihar Nasarawa kuma ma’aikaci ne da ya dade yana ayyukan raya addinin Musulunci kamar gina masallatai da makarantun Islamiyya da sayen filaye yana ba da su a matsayin makabarta, lamarin da ya sa wasu ke ganin kamar yana yin haka […]

Ba don siyasa nake ayyukan raya addini ba – Chakis
Ba don siyasa nake ayyukan raya addini ba – Chakis

Alhaji Shitu Ahmed wanda aka fi sani da Chakis dan gidan sarauta ne a Lafiya Jihar Nasarawa kuma ma’aikaci ne da ya dade yana ayyukan raya addinin Musulunci kamar gina masallatai da makarantun Islamiyya da sayen filaye yana ba da su a matsayin makabarta, lamarin da ya sa wasu ke ganin kamar yana yin haka ne don siyasa. A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana dalilin da ya sa yake yin haka:

Za mu so ka gabatar da kanka
Sunana Alhaji Shitu Ahmed, amma an fi sanina da Chakis. Wannan Chakis din suna ne da abokaina suka ba ni lokacin da muke tasowa muna buga kwallon kafa. Saboda haka idan ka kira Chakis kusan kowa ya san da ni kake, ina aikin gwamnati kuma ina dan taba kasuwanci.
Me ya ba ka sha’awar gudanar da ayyukan raya addinin Musulunci?
Kamar yadda na girma na ga iyayena suna kwatantawa ya sa nake haka, ka san an ce duk abin da mutum zai yi idan ya yi koyi da iyayensa zai ga albarkar wannan abu a karshe. A lokacin da nake tare da mahaifina Malam Shitu na ga irin abubuwa da yake yi. Wadannan ayyuka da nake yi kamar sayen filaye in bayar ana amfani da su a matsayin makabarta da gina makarantun Islamiyya da masallatai da sauransu na gano cewa abin da zan iya yi wa al’ummata ke nan a halin yanzu. Kamar yadda na bayyana maka ni ma’aikacin gwamnatin ne, wata rana ko in ki ko in so, zan yi ritaya daga aiki. Sannan a ce yau na yi ritaya daga aiki babu wani abu da zan iya cewa na yi ga al’ummata in dawo gida in zauna kawai haka bai dace ba. Na biyu kuma ina yin wadannan abubuwa ne don in cika umurnin Allah. Wato in yi abin da Allah Ya ce Musulmi ya yi idan yana da hali, idan ina yin haka ba shakka Allah zai yi farin ciki da ni, Ya kuma kara min arziki. Domin a ganina duk abin da Allah Ya ba ni yau, to, bai ba ni ba don in ci da iyalaina kadai ba. Dole ne in kwatanta in ba al’ummata wani abu kuma in yi ayyukan da za su daukaka addinina wato Musulunci. Kuma a gaskiya ina ganin ci gaba da nasarori sosai a rayuwata sakamakon wadannan ayyuka da nake yi, haka ya sa nake ci gaba da yin su. Kuma insha Allahu in ina da rai to, kamar ma ban fara komai ba.
Wasu na cewa kana yin ayyuka ne don neman sarauta ko mukamin siyasa, me za ka ce?
Ba shakka ina sane da haka mutane da dama suna tunanin haka. To, bari in gaya maka ka ga a masarautarmu ta Lafiya inda na girma, idan ka yi bincike za ka ga cewa duk wadanda ke wurin yau babu wanda ya mallaki Naira miliyan goma na kansa a lokacin da ya samu wannan sarauta. Kuma idan ka lura sha’anin mulki musamman a nan jiharmu Nasarawa za ka ga cewa duk masu mulki yau Allah ne Ya ba su, ba wai kudinsu ko ayyukan da suke yi wa al’ummarsu ba. Saboda haka idan Allah zai ba ni wata sarauta a Lafiya ko wata kujerar siyasa, ba sai na yi wadannan ayyuka ba. Akwai wadanda suka yi irin wadannan ayuka wasu cikinsu ma sun yi fiye da ni, Allah bai ba su mulki ba har suka koma gare Shi. Saboda haka ina so kowa ya sani cewa jahilci ne a ce ina yin wadannan abubuwa ne saboda neman sarauta ko wani abu makamancin haka. Ina yi ne fisabilillahi. Ko Allah Ya ba ni sarauta ko mukamin siyasa ko bai ba ni ba, alhamdullillahi. Wallahi ina yi ne don in faranta wa mahallicina rai ba kowa ba kamar yadda Yake faranta min rai. Kuma ina so in kara da cewa idan mutum ya nace cewa ina yi don neman alfarma, to, ai na kai matsayin da zan iya tsayawa takarar kowane mukami a kasar nan. Yau ina da shekara sama da 50 a duniya kuma iyayenmu ma ba su kai shekaru 40 ba Allah Ya ba su mulki. Saboda haka duk wadannan maganganu ba za su hana ni ci gaba da gudanar da ayyukan da za su daukaka addinin Musulunci ba, sai dai su kara min karfin gwiwa in ci gaba da yi.
Yaya za ka bayyana ci gaban da aka samu a Masarautar Lafiya cikin shekara 40 na Sarkin Lafiya Alhaji Isa Mustapha Agwai?
Mai martaba Sarkin Lafiya a kullum addu’ar da muke masa ita ce Allah Ya bar mana shi cikin koshin lafiya don mu ci gaba da cin moriyarsa. Ya kawo mana ci gaba mai yawa da abubuwan kirki masu dorewa ba ma a masarautar Lafiya kadai ba a jihar nan baki daya. Ba a taba samun wani Sarki da aka samu ci gaban da ake samu irin na wannan zamani na Mai martaba Sarki Isa Mustapha Agwai ba. Ba sai na gaya maka ba ka san yadda ya yi gwargwarmaya har aka kirkiro jihar nan a 1996. Ya rike kowa a jihar nan ba wai mu ’ya’yansa da ke fada kawai ba. Ka ga maganar fadace-fadacen nan Mai martaba ba ya barci yana kai-kawo kullum don tabbatar ya kawo karshen wadannan rigirgimu a jihar nan baki daya. Saboda haka idan zan bayyana ci gaban da Mai martaba Sarkin Lafiya ya kawo jihar nan da kuma wadanda yake ci gaba da kawowa sai mu dauki lokaci mai tsawo ban kare ba saboda suna da yawa. Saboda haka a takaice dai ba domin yardar Allah sannan da kuma kwazon Sarkin Lafiya ba, da ba a ma kirkiro da jihar nan ba balle a yi maganar ci gabanta.
Ko akwai wata kungiya ko gwamnati da ke tallafa maka wajen gudanar da wadannan ayyuka?
Duk ayyukan da ka ga inayi wa al’ummata ban taba tafiya wurin gwamnati ko wata kungiya neman gudunmawa ba. A gaskiya ban tashi cikin talauci ba, kuma ni dan kasuwa ne dan albashina da ribar da nake samu a harkar kasuwancina ne nake amfani da su nake gudanar da wadannan ayyuka, babu wanda yake tallafa min. A duk lokacin da na samu albashi da riba nakan ware na wadannan ayyuka abin da nake yi ke nan da dadewa. Don na lura cewa idan ka tsaya jiran gwamnati ko kungiyoyi su taimaka maka ba za ka bauta wa al’ummarka ba. Gwamma ka sa kai idan Allah Ya ga kokarinka sai Ya taimaka maka. Misali wannan makaranta da na gina da ake shirin budewa kwanan nan makarantar da ake kira Al-Fajarus Sadik wanda ake koyon harshen Larabci da Ingilishi, wadanda ire-irensu suna da yawa a kasar Saudiyya. Na ga ya dace ’ya’yanmu su ma su samu ilimin addini da na zamani ne shi ya sa na gina wannan makaranta ba tare da taimakon gwamnati ko wata kungiya ba. Kuma ba wai fariya ba, Allah ne kadai Ya san irin kudin da na kashe a makarantar. Kuma ina farin ciki da damar da Allah Ya ba ni har na kammala ginin makarantan wadda nan ba da jimawa ba Gwamna Umaru Tanko Al-Makura zai kaddamar da ita.
A karshe wane kira kake da shi ga masu hannu da shuni irinka don gina abubuwan da za su taimaki jama’arsu?
Kamar yadda kullum nake gaya wa jama’a akwai wadanda ke yin irin wadannan ayyuka ba ni kadai ba ne, ba a san wasu ba ne. Wasu na yi ne a boye, mu kuma da muke yi a fili ba wai muna neman yabo ko alfarma ba ne kamar yadda na bayyana a baya. Muna yi ne saboda wasu su yi koyi da mu, saboda haka ina so in yi amfani da wannan damar in yi kira ga duk mai hali da ya zo mu hada hannu mu cigaba da gudanar da irin wadannan ayyuka don kyautata wa ’ya’yanmu da kuma daukaka addinin Musulunci a kasar nan baki daya. Kada kuma mu manta cewa duk arzikinka yau wata rana za ka mutu a saka ka a cikin fallen zani a kai ka bayan gari a kuma saka ka a cikin rami. To, idan ka san da haka me zai sa ba za ka zuba jari daga abin da Allah Ya ba ka a duniyar nan ga ayyukan da za su faranta maSa rai ba don ka samu shiga Aljanna idan Ya kira ka gobe ba?