Ba fulaninmu ne suka tada rikici a Enugu ba – Ardo Sa’idu
Aminiya ta tattauna da Ardon Fulani na kudu maso gabashin kasar nan Alhaji Ardo Sa’idu Baso don jin halin da suke ciki a yankinsu: Aminiya: Ka fadi sunanka da shugabancin da kake da shi.?Ardo Baso :Sunana Alhaji Ardo Sa’idu Baso. ni Ardo ne na Fulani makiyaya na kudu maso gabas. Aminiya: Yaya zamantakewa take tsakanin […]
Aminiya ta tattauna da Ardon Fulani na kudu maso gabashin kasar nan Alhaji Ardo Sa’idu Baso don jin halin da suke ciki a yankinsu:
Aminiya: Ka fadi sunanka da shugabancin da kake da shi.?
Ardo Baso :Sunana Alhaji Ardo Sa’idu Baso. ni Ardo ne na Fulani makiyaya na kudu maso gabas.
Aminiya: Yaya zamantakewa take tsakanin ku fulani makiyaya da kabilun wannan jihar ta Enugu.?
A gaskiya kafin irin wadannan matsalolin su fara tasowa zan iya cewa muna da kyakkyawar alaka tsakaninmu da kabilun wannan jihar a tsawon shekaru talatin da hudu da muke tare, sai da wannan rikici na kwanan nan ya faru.
Aminiya: A jihar Enugu yaya tsakaninku da manoma yake?
Lallai kamar yadda na yi maka bayani yadda muke da kyakkyawar zamantakewa da mu da wadannan kabilun babu batun maganar barnar gonaki a tsakaninmu da su, domin tsakanin manomi da mai shanu ba a yau ba ne irin wadannan kurakuran suke faruwa ba, amma kuma suna tafiya tare babu wata hayaniya, amma wannan matsalar ta yanzu ta kawo mana damuwa kwarai.
Aminiya: Akwai wadansu matakai ne da kuka dauka?
Babu wasu mataki na daban da muke dauka, illa kawai idan muka ga wani abu zai kawo mana damuwa da mu da su, sai mu kira juna mu tattauna a kan duk wata matsala da ta taso domin warware ta a cikin sauki.
Aminiya: kwanakin nan wadansu mahara sun far wa kauyen Akpabi-Nimbo a cikin karamar hukumar Uzo-uwani, kuma ana zargin mutanenku fulani da kai wannan harin, wane bayani za ka yi?
A gaskiya hakan ya faru, amma kuma iya abin da na sani wannan ta’asar babu hannun bafulati mazunin Enugu a ciki, don haka muna tir da wannan rashin hankali na masu aikata ta’addanci a kasar nan, kuma ina ganin akwai sakaci daga hukumar ‘yansanda da ba ta daukar mataki kafin faruwar lamari, amma a daina alakanta aikin ta’addanci ga fulani.
Aminiya: Mene ne hujjarka cewa ba Fulani ne suka aikata wannan ta’assar ba.?
Kamar yadda na gaya maka, sam mu fulani mazauna nan Enugu ba mu da alaka da ko wace kungiyar ta’addanci, don haka muna Allah wadai da wannan aika-aikar.
Aminiya: Akwai majiyar da ke cewa ramuwar gayya mutanenku suka yi, domin akwai fulanin da aka kashe har da wani shugabansu a ciki awannan yankin, gaskiya ne hakan ya faru.?
Ni ma abin da na ji ke nan, an ce akwai yaran wadansu bakin fulani wadanda mu ba mu san da su ba da aka kasha, har da wani tsoho a ciki, wannan ya sa watakila ake alakanta wannan harin na Nimbo da cewa wai fulani ne suka yi ramuwar gayya.
Aminiya: Me za ka bayyana game da umarnin da shugaba Buhari ya bayar da ya ce wa jami’an tsaro su bincika su gano wadannan da suka aikata wannan kisan da sauran masu miyagun ayyukan?
Wallahi ina goyon bayan gwamnati dari bisa dari, duk wanda aka samu da hannunsa a wannan kisan na kauyen Akpabi Nimbo to a zartar masa da hukunci daidai da laifinsa, sai dai abin da ban goyi bayansa ba shi ne a je a kama wanda bai san hawa da sauka ba a wulakanta shi ko a kasha shi saboda kabilanci ko siyasa.