Ba gagararre sai bararre
A ’yan kwanakin nan an kai munanan hare-hare kan wasu wuraren hakar mai da bututun sarrafa shi mallakar kamfanonin kasashen waje na Shell da Chebron da Agip da kuma na NNPC, na nan cikin gida. Wata kungiyar ’yan ta’addar yankin Neja Delta da ake kira Abengers, mai ra’ayin ballewa daga Jamhuriyar Najeriya ce ta dauki […]
A ’yan kwanakin nan an kai munanan hare-hare kan wasu wuraren hakar mai da bututun sarrafa shi mallakar kamfanonin kasashen waje na Shell da Chebron da Agip da kuma na NNPC, na nan cikin gida. Wata kungiyar ’yan ta’addar yankin Neja Delta da ake kira Abengers, mai ra’ayin ballewa daga Jamhuriyar Najeriya ce ta dauki alhakin kai hare-haren. Kodayake Gwamnatin Tarayya ta nemi ’yan kungiyar Abengers da su zauna da ita don tataunawa, amma sun kekasa, sun ki, sun ce babu abin da suke bukata illa ballewar yankin Kudu-Kudu daga tarayyar Najeriya.
To, tun daga lokacin da aka bayyana gagarumar asarar da ake samu dangane da hare-haren, sai ’yan ta’addan suka kara dukufa wajen rugurguza butun man ba kakkautawa, kuma sai hakan ya yi ta kara rage yawan man da ake hakowa a kunllum. Wannan al’amari ya shafi aikace-aikacen kamfanonin hakan mai da kuma yadda ake fitar da man don sayarwa, domin kuwa hudu daga cikin manya-manyan wuraren fitar da man guda biyar zuwa kasashen ketare sun daina aiki gaba daya.
A sakamakon haka nan, an samu matsaloli game da samar da karfin wutar lantarki wanda ya tabarbare ainun, har ma sai da ta kai ba a samar da rabin adadin da ake samarwa. Bayan haka nan kuma ta’addacin ya kai hatta ma kudin man da ake fitarwa, ana sayarwa a kasashen ketare don samun kudin da za a kasafta wajen gudanar da al’amura da ayyukan gwamnatocin kasar nan yana raguwa da misalin ganga dubu dari takwas, cikin ganga miliyan biyu da dubu dari biyu da aka saba hakowa a kullum. dimbin asarar da hare-haren ya janyo a bangaren hakan mai ya kai Naira miliyan dubu dari da daya a cikin kwanaki-sha- uku kadai, tun daga ranar goma sha shida ga watan jiya, kaman yadda Minista a Ma’aikatar Man Fetur, Dokta Ibe Kachukwu ya tabbatar.
Idan aka yi la’akari da farashin gangar danyen mai a kasuwannin duniya akan dalar Amurka arba’in da tara a yanzu, aka kuma lura da cewa farashin dala ta kai Naira dari da casa’in da bakwai sai a fahimci cewa kudaden da za a samu daga gangunan danyen mai da hare-haren ya hana a hako har guda dubu dari takwas a kullum na da yawan gaske. karuwar ta’addancin farfasa bututun mai a wannan shekarar ya haddasa gagarumar hasarar kudade ga Gwamnatin Shugaba Buhari, wacce ta gaji mulki cikin tsananin rashin kudi da kuma tabarbarewar al’amuran da ake matukar bukatar kudade don magancewa. Najeriya dai ta dogara ne kacokan kan danyen mai wajen tallabar tattalin arzikinta, to tun da kuwa haka abin ya kasance ashe tangardar da za a iya samu game da yawan man da take fitarwa don sayarwa, ko kuma faduwar farashinsa a kasuwannin duniya, za su iya janyo mata manyan matsalolin da za su gallabe ta. Shi ya sa a nan cikin gida da kuma kasashen ketare ake ganin wadannan hare-haren da ’yan ta’addan Abengers ke kaiwa tamkar zagon kasa ne ga tattalin arzikin kasar nan wanda ya dade yana tangal-tangal.
Ta’adin da dai aka yi a wuraren hakan man da kuma irin gyararrakin da za a yi, hade da canja sabbin bututun da aka lalata ba ‘yar kadan ce ba, kuma za a kashe makudan kudade, a kuma dauki dogon lokaci kafin a mayar da su yadda suke tun can farko. daya daga cikin wuraren da aka lalata na samar da gangan danyen mai dubu dari biyu da hamsin a kullum, wadanda ake lodawa bisa jiragen da ke ketarewa da su kasuwannin waje don sayarwa. A sakamakon haka masu sayen danyen man Najeriya a kasashen waje na dari-dari wajen sayen mai daga Najeriya don gudun jinkirin kawowa ko kuma rashin man gaba daya. danyen mai daga Najeriya, da ake kira Bonny Brent, ya fi na sauran kasashen duniya kyau da daraja da kuma tsada. A yanzu akan sayar da ganga guda na danyen man Najeriya akan dalar Amurka arba’in da takwas zuwa hamsin. Amma abin ban Haushi shi ne ga bukin zuwa amma ba zanin daurawa. Ga shi dai farashin danyen man da Najeriya ta yi kasafinta na bana a bisa farashinsa na dala talatin da takwas, ya haura zuwa kusan dala hamsin, amma ba dama ta amfana da tashin farashin domin ba ta fitar da adadin da ta kasafta a bana na ganga miliyan biyu da dubu dari biyu a kullum. Wannan abin takaicin da mene ya yi kama? Irin haka ne ake kira ga koshi, ga kuma kwanan yunwa. A bana dai Najeriya ta kiyasta cewa za ta samu kudin shiga har sama da Naira miliyan duibu dari takwas da shirin, amma da wuya ta samu haka saboda ta’addancin da aka yi da gangan don gurgunta tattalin arzikinta, kuma idan ba a kawo karshensa ba da gaggawa al’amarin zai kara kazancewa, har ta kai an karasa gurgu da tadiye..
Amma a wani jawabin da ya yi daukacin al’ummomin kasar nan ta kafafen yada labarai da sanyin safiyar Lahadin da ta gabata, Shugaba Muhamadu Buhari ya ce za a dukufa wajen gano masu aikata ta’addancin farfasa butu da kuma lalata wuraren hakan mai a yankin Neja Delta, za a kuma binciko ko su wane ne ke daure masu gindi suna aikata ta’asa irin haka, a kuma hukunta su ta yadda za su dandana kudarsu. Shugaba Buhari ya ce idan ’yan ta’addan da kuma tsagerun yankin Neja Delta sun ce kule, gwamnati kuma za ta ce da su cas, a ga wanda zai fasa. Ko da yake an ce wai ‘yan Abengers sun nuna alamun saduda, suna so a sulhunta tsakaninsu da gwamnatin tarayya, amma ai ba a saurin yabon dan kuturu sai an ga ya girma da yatsunsa.
Wajibi ne fa a tunkari ’yan Abengers tun da wuri, don kada wankin hula ya kai maraice, a bari har sai sun gawurta, sun kasara, kuma yakansu, ko maganinsu ya gagara cikin sauki, kaman yadda ake fama da kungiyar Boko Haram a halin yanzu. Shugaba Buhari ya kyauta da ya fito fili, ya nuna masu cewa ba fa za a kyale su, su yi yadda suke so ba, su kuma gurgunta tattalin arzikin kasar nan haka nan ba. An ce ba a san ko su wane ne su ba, tun da ba a ganinsu, sai dai a ga ta’adin da suka tafka. To amma ai su ba rauhanai ne ba, ba kuma iskokin boye ne ba, mutane ne masu jini a jika, wadanda kuma ke son tayar da fitinar da za ta buwayi kowa da kowa, ta kuma jefa kasar cikin wagegen ramin da za ta kasa fitowa. To an ce katala muzika, kabla an yazika. Wajibi ne a fafare su, har sai an ga bayansu, domin kuwa babu wani gagararre sai bararre.