Ba gina Ruga ne mafita ga makiyaya ba – Sheikh Bawa Kafanchan

Shugaban Majalisar Malamai ta Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah reshen Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna Malam Bawa Ibrahim Kafanchan ya ce ba shirin gina rugage da ya tayar da kayar baya da Shugaban Kasa ya janye daga baya ba ne mafita ga matsalar da ke fuskantar makiyaya, sai dai maimakon haka a tanadar […]

Ba gina Ruga ne mafita ga makiyaya ba – Sheikh Bawa Kafanchan

Sheikh Bawa Ibrahim Kafanchan

Shugaban Majalisar Malamai ta Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah reshen Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna Malam Bawa Ibrahim Kafanchan ya ce ba shirin gina rugage da ya tayar da kayar baya da Shugaban Kasa ya janye daga baya ba ne mafita ga matsalar da ke fuskantar makiyaya, sai dai maimakon haka a tanadar musu da labi-labi da hanyoyin da aka san suna bi da dabbobinsu a kowane yanki da ke sassan kasar nan.

Sheikh Bawa Ibrahim ya bayyana haka ne yayinda yake tattaunawa da Aminiya a garin Kafanchan, inda ya ce kasancewar kowane lokaci akwai yankin da dabbobin suka fi samun saukin kiwo abin da ya sa makiyaya ba sa zama a wuri daya, zai fi kyau gwamnati ta tilasta duk wadanda suka toshe hanyoyin da tun lokacin Turawa Fulani makiyaya ke amfani da su su bude ta hana su yin gine-gine ko nomewa;  a bar wa makiyaya hanyoyinsu tunda shirin gina rugage bai ci nasara ba.

“Ta yiwu tunda farko Shugaban Kasa ya ji shawarar wadansu ne kan neman mafitar da ake yi tsakanin rikicin manoma da makiyaya kan gina rugagen sannan daga baya wadansu kuma suna sake ba shi shawarar janyewa. Duk dai abin da ake nema shi ne abin da zai zamo mafita da samar da zaman lafiya,” inji shi

Da yake tsokaci kan matasa kuwa, shugaban ya yi kira ga ’yan Najeriya musamman matasa su daina jiran sai sun samu aikin gwamnati; alhali ga manya da kananan sana’o’i nan da mutum zai runguma don samun rufin asiri.

“Kowa yana jin yadda gwamnati ke kukan abubuwa sun yi mata yawa ba kuma za ta iya wadatar da kowa ba, to me zai sa ka tsaya jiran sai gwamnati ta dauke ka aiki alhali kofofin Allah na da yawa, kuma hanyoyin nema na da yawa? Baya ga aikin gwamnati akwai sana’o’i da yawa da kasuwanci da noma da  kiwo kowane daga ciki yana da albarka sai mutum ya gwada ya ga wanda ya karbe shi,” inji shi.

Malamin, wanda ya yi kira ga gwamnati ta bai wa matasa kula ta musamman wajen ba su ilimi ingantacce kuma cikin sauki, ya yi kira ga al’ummar Najeriya Musulmi da Kiristoci su koma ga karantarwar addinansu kamar yadda ya ke cikin littattafansu don samun mafita daga halin rashin kwanciyar hankali da yawaitar ayyukan assha da suka dabaibaye al’umma.