Ba gudu ba ja da baya kan fara yajin aiki – ’Yan ƙwadago

Kungiyar ta ce sam ba ta tattauna da gwamnati ba kan batun

Ba gudu ba ja da baya kan fara yajin aiki – ’Yan ƙwadago

Zanga-zangar NLC

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta ce sam ba ta yi wata tattaunawa da Gwamnatin Tarayya da za ta sa ta janye yajin aikin da ta kuduri aniyar farawa ranar Talata ba.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar take shirye-shiryen fara yajin aikin domin nuna rashin jin dadinta kayan manufofin tattalin arziki na Gwamnati mai ci, musamman janye tallafin man fetur.

Majalisar kungiyar, ta bakin jami’in yada labaranta, Benson Upah, a ranar Alhamis ta ce bukatunta sun fi karfin Ministan Kwadago, Simon Lalong.

Sai dai ya ce sun jinjina wa rawar da Lalong din ya taka wajen fito da shugabannin Kungiyar Direbobi ta Kasa (NURTW) kan abin da suka kira kamun da aka yi musu ba bisa ka’ida ba.

Idan za a iya tunawa, kungiyoyin NLC da TUC sun umarci dukkan rassansu da su kulle komai a Najeriya daga ranar Talata saboda kin mutunta bukatunta.

Yajin aikin dai na sai baba-ta-gani ne har sai gwamnati ta biya musu bukatun nasu da suka hada da karin albashi da sassauta harajin da ma’aikata ke biya.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja