‘Ba hannun Fulani cikin kai hare-hare a kauyukan kasar nan’

Shugaban kungiyar Miyetti Allah Ta Nijeriya, Alhaji Muhammad Kiruwa, Ardon Zuru, ya nisanta Fulani da hannu a cikin kashe-kashen da ake yi a wasu sassan kasar nan, “Ba hannun Filani ga kai hare-hare a kauyukkan kasar nan, zargi ne maras tushe kawai ake yi domin rena mutanenmu da aka yi, bayan kowa ya san an […]

‘Ba hannun Fulani cikin kai hare-hare a kauyukan kasar nan’
‘Ba hannun Fulani cikin kai hare-hare a kauyukan kasar nan’

Shugaban kungiyar Miyetti Allah Ta Nijeriya, Alhaji Muhammad Kiruwa, Ardon Zuru, ya nisanta Fulani da hannu a cikin kashe-kashen da ake yi a wasu sassan kasar nan, “Ba hannun Filani ga kai hare-hare a kauyukkan kasar nan, zargi ne maras tushe kawai ake yi domin rena mutanenmu da aka yi, bayan kowa ya san an yi ta kama wasu mutane a Kaduna da Jos wadanda ba Fulani ba, amma har yanzu ba a daina tsangwamarmu ba, wanda hakan rashin adalci ne ake yi mana.”
Shugaban ya yi wadannan kalamai ne a ranar Litinin a Jihar Sakkwato jim kadan bayan rushewa tare da nada sabbin shugabannin rikon kwarya na kungiyar, reshen Jihar Sakkwato a dakin taro na otal din Giginya.
Shugaba Kiruwa ya ce, “Mun zabi sabbin shugabanni ne domin su tsaftace kungiyar reshen jiha don samar da cigaban dalilan da aka kafa kungiyar, wanda ya hada da wayar da kan Fulani makiyaya kan dokokin kasa don kiyayewa; da kuma samun hadin kai tsakanin dukkan Fulani a duk inda suke; da nema wa ‘ya’yansu hakkinsu duk inda yake; da tabbatar da sun samu ilimin zamani da na addini don kauce wa samun matsala ta raba su da addini da ake yi a wannan kasar.”
Don haka ya ce wa Shugabannin, “Kuna da kulabale a gabanku wajen jajircewa kan kokarin sauya kungiyar Miyetti Allah ta Jihar Sakkwato, wadda ita ce zuciyar ta kasa.”
Shugaban ya yi kira ga sauran Fulani da ba su cikin kungiya saboda wani dalili na kashin kansu da su watsar da shi domin zuwa a tafi tare don fuskantar kowane irin kalubale a kasar nan.
Alhaji Kiruwa, bayan ya kaddamar da sabbin Shugabannin, ya yi kira gare su da su ji tsoron Allah a cikin lamurransu, musamman wajen samar da hadin kai a tsakanin mambobin kungiya, domin bangaranci ya kare a tsakanin Fulani.
Shugabannin aka zaba, wadanda za su gabatar da zabe bayan kwanaki 90 domin samun shugabanni masu cikakken iko, sun hada da Alhaji Jeli Abubakar na Uku, Dikkon Sakkwato, a matsayin Shugaba da Barista Garba Jedo Gidan Madi, Sakatare da Muhammad Mijinya, Ma’aji da Hajiya Hauwa, Shugabar mata da kuma Muhammad Maishanu, a matsayin jami’in hulda da jama’a.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno