Ba hannunmu a jirkita dokar Majalisar Dattawa – Akawu da Mataimakinsa

Akawun Majalisar Dokoki ta kasa mai barin gado, Alhaji Salisu Maikasuwa da Mataimakinsa Ben Efeturi, sun ce babu hannunsu a jirkita dokar gudanar da Majalisar Dattawa, inda suka ce shugabannin majalisar ne suka yi haka. Wannan labari na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar ta yi sammacin Minsitan Shari’a, Abubakar Malami game da shari’ar […]

Ba hannunmu a jirkita dokar Majalisar Dattawa – Akawu da Mataimakinsa
Ba hannunmu a jirkita dokar Majalisar Dattawa – Akawu da Mataimakinsa

Akawun Majalisar Dokoki ta kasa mai barin gado, Alhaji Salisu Maikasuwa da Mataimakinsa Ben Efeturi, sun ce babu hannunsu a jirkita dokar gudanar da Majalisar Dattawa, inda suka ce shugabannin majalisar ne suka yi haka. Wannan labari na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar ta yi sammacin Minsitan Shari’a, Abubakar Malami game da shari’ar jabun dokar majalisar. 
Maikasuwa da Efeturi a bayanansu daban-daban ga ’yan sanda sun musanta cewa suna da hannu a batun jabun dokar. Bayanansu na kunshe ne a cikin takardar sammacin kotu da aka lika a allon Majalisar Dokoki ta kasa da ke bukatar Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki da Mataimakinsa, Ike Ekweremadu su bayyana a gaban kotu don kare kansu kan shari’ar jabun dokar.
Umarnin kotun na ranar 21 ga Yuni, dauke da lambar kara: Cb/219/16 ya ce: “Umarnin wannan kotu mai martaba na amincewa a mika sammaci ga wadanda ake kara ta hanyar lika ta a allon Majalisar Dokoki ta kasa da ke yankin ginin majalisa.” Na dauke ne da sa hannun D.E.Kaswe, Babban Lauya a Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya.
Maikasuwa a rubutun hannunsa ya ce: “Dokar Gudanar da Majalisar Dattawa da aka yi amfani da ita a majalisa ta bakwai, ban san ta ba. Kuma abu ne da wajibi ne Akawun Majalisar Dattawan ya sani. Ban san an yi gyara ga dokar gudanar da majalisar ba.”
Shi ma a bayaninsa, Efeturi ya ce shugabannin majalisa ne suka mika dokar gudanar da majalisa ta shekarar 2015, kamar yadda suka gyara. “Shugabannin Majalisar Dattawa ne suka mika dokar majalisar ta 2015 kamar yadda suka gyara bisa taronsu da al’adarsu. Dokokin gudanarwar na 2003 da 2007 da 2011 ma haka aka yi,” inji shi.
Majalisar a wata sanarwa a baya da Sanata Aliyu Sabi Abdullahi (APC, Neja ta Arewa) ya fitar, ta ce shugabannin gudanar da majalisar ne suka mika musu dokokin.
Sanata Dino Melaye (APC, Kogi ta Yamma) ne ya gabatar da bukatar a majalisar ta yi sammacin Minista Malami kuma ya bayyana a gabanta cikin awa 48, duk da tsohon shugaban majalisar Sanata Dabid Mark ya yi gargadi kan hakan. Majalisar ta amince da kudirin da ke nuna cewa dokokin gudanar da majalisar ba na jabu ba ne.
Batun ya jawo takun-saka a tsakanin banagren majalisa da na zartarwa inda Majalisar Wakilai ta ce matakin shari’ar kai hari ga bangare majalisa daga bangaren zartawa, yayin da sanatocin PDP 49 suka ce sun janye goyon bayan da suka ba Shugaban kasa Buhari, kamar yadda kakakinsu Sanata Emmanuel Bwacha ya bayyana wa manema labarai ranar Talata a Abuja.

Daga Ismail Mudashir da Clement A. Oloyede da Salihu Makera