‘Ba Hausawa kadai masarautar Hausawan Ojora take mulki ba’’
kabilu daban-daban har da Yarabawa da ke zaune a Masarautar Hausawan Ojora da ke Legas, sun nuna matukar farin cikinsu da irin salon mulki da Sarkin Hausawan Ajeromi Ifelodun, Alhaji Adamu Abubakar Naby yake gudanarwa wajen sasanta al’amuransu ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba. “Wannan Sarki shi ne yake tashi cikin dare […]
kabilu daban-daban har da Yarabawa da ke zaune a Masarautar Hausawan Ojora da ke Legas, sun nuna matukar farin cikinsu da irin salon mulki da Sarkin Hausawan Ajeromi Ifelodun, Alhaji Adamu Abubakar Naby yake gudanarwa wajen sasanta al’amuransu ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba.
“Wannan Sarki shi ne yake tashi cikin dare ko rana da ruwa ya saurari koke-koken jama’a da suka shafi daurin aure da rabon gado da matsalar bashi a tsakanin ’yan kasuwa da makamantansu,” inji wani Bayarabe dan kasuwa mai suna Festus Onalapo da ke gudanar da harkokinsa a cikin masarauntar ta Ojora.
A wata hira da wakilinmu, Festus ya ce Sarki Adamu shi ne yake amfani da kudin aljihunsa wajen sasanta tsakanin talakawansa ba tare da ya caje su ko kwabo ba. “Irin wadannan shugabanni muke bukata wajen yin shugabanci ba tare da kwadayin abun hannun talakawansu ba.” Inji shi.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Sarkin Hausawan game da irin salon mulkinsa, ya ce: “Bayan godiya ga Allah (swt), ina tabbatar maka cewa ina yin koyi ne da marigayi Sarkin Hausawa, Onuh na Igala na Jihar Legas, Alhaji Ibrahim Akoh dangara, wanda kabilun Arewacin kasa da Yarbawa da Ibo mazauna masarautar Ojora suka ci moriyar mulkinsa ba tare da bambanci ba. Ni ma irin wannan salon mulki nake yi, wanda ya sa wasu mutane suke danganta zuriyata da kabilun Yarbawa amma babu abun da ya hada ni da su, domin ni dai Bahaushe ne dan asalin Jihar Kano. Duk da yake ban gaji wannan sarauta ba amma mahaifina Abubakar Abdullahi, kafin rasuwarsa ya yi aiki a matsayin manaja a Hukumar Kula da Noman Auduga ta Najeriya. Shi kuma kakana Malam Abdullahi, shi ne Jakadan Koya, da ya yi wakilci a karkashin marigayi Sarkin Kano Sanusi yana hakimi a lokacin. Su ma mahaifana uwa da uba sun fito ne daga gidan Kwando a garin Kunya cikin karamar Hukumar Minjibir a Jihar Kano. Zaman kasuwanci ne ya kai su suka haife ni a Legas shekaru 60 da wucewa kuma na yi karatu zuwa Jami’ar Legas kafin in shiga aikin sojan ruwa.”