Ba-Jamushiya ta shekara ba ta kashe kudi ba

Wata Bajamushiya, Greta Taubert ta jarraba rayuwar shekara guda ba tare da kashe kudi ba. Wannan mata ’yar shekara 30, ’yar jarida ce, wadda tunaninta ya damfaru da son gano yadda rayuwa za ta kasance idan aka samu matsalar tattalin arziki, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.Da farko dai ta fuskanci matsala, […]

Ba-Jamushiya ta shekara ba ta kashe kudi ba
Ba-Jamushiya ta shekara ba ta kashe kudi ba

Wata Bajamushiya, Greta Taubert ta jarraba rayuwar shekara guda ba tare da kashe kudi ba. Wannan mata ’yar shekara 30, ’yar jarida ce, wadda tunaninta ya damfaru da son gano yadda rayuwa za ta kasance idan aka samu matsalar tattalin arziki, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.
Da farko dai ta fuskanci matsala, saboda ita ma’abociyar shan gahawa ce, abin da ta saba sha a birnin Leipzig da ke Gabashin Jamus.
“Sabulun wanka da wanki a bandaki,” al’amuran da ta bayyana cewa tana matukar bukata don kula da gashin kanta. Ta kirkiro wa kanta sabulu da man shafawa da abin goge baki, wadanda duk daga tsirrai ne, dari bisa dari.
“Har gyaran gashi na rika yi da shamfo,” inji ta. “amma fa na fara sauya kammanu na kamar kirar mutanen da, wadanda suka bace. Abokaina sun bayyana mini cewa, “na kai makura a tsanantawa,” a cewarta, in data rika yin dariya.
Tsawon shekara guda, Taubert ’yar jarida mai zaman kanta ta rika sauya tufafi a wurin da ake ajiye kwancen tufafi, sannan ta gyara kasar noma, inda ta yi lambu da take noman kabeji da dankali.
A duk lokacin da take sha’awar zuwa wani garin don shakatawa, sai ta fara tataki a kasa, ko kuma ta rika rokon masu ababen hawa su rage mata hanya, har ta kai ga ta shafe kilomita dubu da 700 daga birnin Barcelona.
Bayan da ta jajirce har tsawon shekara daya ta cikin irin wannan hali, sai kawai ta rubuta wani littafi mai taken Sirrin Bajumushiya – German for Apocalypse.”
Taubert ta fara fafutikar kyautata muhali ne a tsakar ranar wata Lahadi, inda a gidan kakarta, ta fara tababar cin kayan makwalshe, wadanda suka hada da biskit da gahawa
“Da na ce ina bukatar madara, sai kakata ta zuba mini garin madara da cakulan da ayaba da sinadaran abubuwa masu inganta dandano wadanda suka ahda da banilla da strawberry,” inji Taubert.
“Tattalin arzikinmu na tafiya ne a kan tsarin hauhawa mara iyaka, amma muhallinmu yana da iyaka,” kamar yadda ta rubua a cikin littafinta, cewa : “kwakwazon bukatar kari, kari, a karo, a karo, al’amarin da ba zai kai mu ko’ina ba,” a cewarta.
A shekarar 2012, kimanin ton miliyan bakwai na abinci aka yi asararsa, da aka zubar a shara, kuma a kalla mutum guda na zubar kilo 81.6.
Al’amuran da ta bijiro da su a cikin littafinta sun tabbatar da abin da wasu marubutan Birtaniya, Robert da Edward Skidelsky suka wallafa, mai taken “Nawa ne zai wadatar – How much is enough? Marubutan sun tabbatar da cewa zamanin da ake ciki bukatun duniya sun yi wa mutane yawa, ta yadda ake ta fafutikar tara kudi abubuwan rayuwa.
Ta karkare littafinta da kokarin tabbatar da cewa za ta rika amfani da darasin da ta koya a tsawon wannan lokaci. “Amma duk da haka ina cike da farin ciki tunda manufata ba ta tsananta ba,” inji ta.