Ba kora ta aka yi daga aikin soja ba – Mawaki Prince Suleiman

Suleiman Ibrahim fitaccen mawakin Hausa ne, a zantawarsa da Aminiya kwanakin baya ya bayyana dalilin da ya sa ya ajiye aikin soja da dalilinsa koma wa fagen kade-kade da wake-wake. Ga yadda hirar ta kasance:Tarihina a takaiceAssalamu alaikum, sunana Suleiman Ibrahim amma an fi sanina da Prince Suleiman, saboda na fito daga gidan sarauta. An […]

Ba kora ta aka yi daga aikin soja ba – Mawaki Prince Suleiman

Suleiman Ibrahim fitaccen mawakin Hausa ne, a zantawarsa da Aminiya kwanakin baya ya bayyana dalilin da ya sa ya ajiye aikin soja da dalilinsa koma wa fagen kade-kade da wake-wake. Ga yadda hirar ta kasance:
Tarihina a takaice
Assalamu alaikum, sunana Suleiman Ibrahim amma an fi sanina da Prince Suleiman, saboda na fito daga gidan sarauta. An haife ni a Jihar Kano cikin shekarar 1975, na yi karatun firamare da sakandare a makarantar Kings Commercial College da ke Kano. Daga nan na wuce Kwalejin Horar da Malamai da ke Jihar Kogi (Kogi State College of Education), Ankpa inda na samu difloma a bangaren Kimiyyar Zamantakewa (Sociology) a cikin shekarar 1994.
Daga nan a shekarar 1997 na shiga aikin soja a Zaria. Bayan wani lokaci kuma na bar aikin, na fada harkar kade-kade da wake-wake.
Dalilina na barin aikin soja
Mahaifiyata ce ta bukaci na ajiye aikin. Amma a gaskiya ba kora ta aka yi ba, umarnin mahaifiyata na bi, saboda an ce bin na gaba bin Allah.
Dalilin da ya sa na fara harkar kade-kade da wake-wake
Ra’ayi ne da sha’awa ya sa na shiga harkar, kuma Alhamdulillahi kwalliya na biyan kudin sabulu. Amma hakan  ba ya rasa nasaba da irin gudunmuwar wake-waken da na bayar a lokacin da nake Gidan Soja, a lokacin  idan muna atisaye na kan taimaka da wakoki irin na karfafa wa sojoji gwiwa a fagen-daga, wannan ya taimaka mini matuka, saboda na sha kirkirar waka, kuma duk lokacin da na gabatar da ita sai ka ga ta samu karbuwa.
kalubale
Ba a raba rayuwa da kalubale amma Alhamdulilah muna kokarin ganin hakan bai sa mun karaya ba a kodayaushe.
Wakokina
Su ne ‘Morale’ da ‘I lobe Nigeria’ da dai sauransu. A kalla za su kai guda 500. Ina da kuma kundin wakokina kamar su ‘Mai Sukus’ da dai sauransu.
Bakandamiyata
Dukkan wakokina, amma jama’a sun fi maganar ‘Morale’ wato wakar da na yi kan Gidan Soja.
Burina
Na samu abun da zan rufa wa kaina asiri, na fi karfin cikina da bukatar iyalina.