Ba ku da damar canja jadawalin zabe- Kotu ga Majalisa

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da batun cewa Majalisa na da damar canja jadawalin zabe ta hanyar dakatar da canjin da majalisar ta yi wa sashe na 25 na kundin zaben. Da yake yanke hukuncin a ranar Laraba, mai shara’a Ahmed Mohammed ya ce Hukumar zabe ta INEC ce kadai ke […]

Ba ku da damar canja jadawalin zabe- Kotu ga Majalisa

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da batun cewa Majalisa na da damar canja jadawalin zabe ta hanyar dakatar da canjin da majalisar ta yi wa sashe na 25 na kundin zaben.

Da yake yanke hukuncin a ranar Laraba, mai shara’a Ahmed Mohammed ya ce Hukumar zabe ta INEC ce kadai ke da damar tsara yanayin zaben kasar nan.

Hakanan kuma, alkalin ya kara da cewa duk wani yunkurin canja jadawalin zaben ba zai yiwu ba sai an fara canja kundin tsarin mulkin kasar nan baki daya.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram