Ba laifi ba ne yi wa mutum kyautar kujerar hajji – Shaikh Sambo
Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum ya bayyana cewa, ba laifi bani a yi wa mutum kyauta, ba kuma laifi ba ne bai wa mutum sadakar kujera hajji, domin idan aka tafi kasa mai tsarki, kasar nan ake wa addu’ar zaman lafiya da cigaba. ‘’Saboda haka abin da nake son gwamnatin nan ta jaha da kuma ta […]
Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum ya bayyana cewa, ba laifi bani a yi wa mutum kyauta, ba kuma laifi ba ne bai wa mutum sadakar kujera hajji, domin idan aka tafi kasa mai tsarki, kasar nan ake wa addu’ar zaman lafiya da cigaba. ‘’Saboda haka abin da nake son gwamnatin nan ta jaha da kuma ta kasa ta sani shi ne, malamai na daya daga cikin mutanen da suka yi gwagwarmaya wajen ganin an samu wannan canji da aka samu a yanzu. Don haka babu laifi idan aka dauki dan kujerar nan na hajji da aka saba ba su domin su ma su amfana da gwamnatin. Tun da da su malaman aka sha wahala wajen neman wannan canji na gwamnati a kasar nan da jaha. Ya kamata a ce su ma akwai wani abin da suke amfana da shi a wannan gwamnati. Ba zan ce kuskure ne kai tsaye ba wannan mataki da ta dauka, amma dai akwai bukatar ta duba, domin idan aka hana a yanzu, ta wacce hanya su malaman za su amfana da ita gwamnatin nan?’’