Ba ma ƙalubalantar hurumin Gwamnatin Kano na naɗawa ko sauke Sarki — Kotu
Kotun na da hurumi game da duk wani al’amari da ya shafi tauye hakkin dan kasa a kowane lamari.
Wata Babbar Kotun Tarayya a Kano ta ce ba ta ƙalubalantar damar da gwamnatin jihar ke da ita na naɗawa ko sauke sarki.
Sai dai kotun ta yanke hukuncin cewa tana da hurumin sauraron ƙarar da aka shigar kan rikicin Masarautar Kano, musamman kan abin da ya shafi kare hakkin ɗan Adam bisa dogaro da sashe na 46 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
- ’Yan sanda sun haramta Hawan Sallah a Kano
- Tinubu da Shettima sun kashe N5bn a tafiye-tafiye cikin watanni uku
Alƙalin kotun, mai shari’a Liman Mohammed na Babbar Kotun Tarayyar da ke jihar, ya yanke hukuncin cewa Sarki Aminu Ado Bayero na da damar a saurare shi a kotu.
Sai dai alkalin ya ce ba magana ce a kan cancantar majalisar dokokin jihar na sauya dokar masarautun jihar ko kuma akasin haka ba.
Babbar Kotun Tarayyar ta ce ta gamsu da hujjojin ta masu kara suka gabatar, saboda haka tana da hurumin sauraron shari’ar taƙaddamar sarautar Kano da za a soma gobe Juma’a.
Alhaji Aminu Babba Danagundi, Sarkin Dawaki Mai Tuta kuma guda cikin masu naɗin sarki a Masarautar Kano ne ya shigar ta ƙara yana kalubalantar rushe masarautu huɗu na Kano da kuma sauke sarakuna guda biyar na Jihar Kano.
Mai Shari’a Muhammad Abdullahi Liman ya ce kotun ta gamsu da hujjar da lauyan Babba Danagundi cewa, matakin Majalisar Dokokin Kano da na gwamnatin Jihar Kano game da sauke sarakunan ya ci karo da ’yancinsa.
Ana iya tuna cewa, a ranar 23 ga watan Mayu ne gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun Kano ta 2024, bayan majalisa ta amince da ita.
Wannan ne ya bayar da damar komawar sarkin Kano na Muhammdu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16 tare da cire Aminu Ado Bayero daga kan mulki.
Sai dai jin kaɗan bayan haka ne Aminu Babba Danagundi ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar sabuwar dokar, inda kotu ta bayar da umurnin tsayawa kan matsayin da ake.
Sai dai lamarin ya janyo ruɗani, inda Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II kowannensu ke iƙirarin shi ne halastaccen sarki.