Ba ma fargabar dawowar Atiku PDP, Inji masu neman takarar shugabancin kasa

  Manyan ’yan jam’iyyar PDP wadanda ke neman jam’iyyar ta tsayar da su takarar shugaban kasa sun mayar da martani kan dawowar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar jam’iyyar don neman tikitin takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019, inda suka ce ba su firgita ba. A ranar Juma’a ne Atiku ya fice daga jam’iyyar […]

Ba ma fargabar dawowar Atiku PDP, Inji masu neman takarar shugabancin kasa

 
Manyan ’yan jam’iyyar PDP wadanda ke neman jam’iyyar ta tsayar da su takarar shugaban kasa sun mayar da martani kan dawowar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar jam’iyyar don neman tikitin takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019, inda suka ce ba su firgita ba.
A ranar Juma’a ne Atiku ya fice daga jam’iyyar APC inda ya zargi jam’iyyar da yi wa ka’idojin damokradiyya karen-tsaye tare da rashin cika alkawuran da suka yi wa ’yan Najeriya.