Ba ma fargabar rikicin siyasa a Kudu – Alhaji Adamu Marke
Daya daga cikin shugabannin ’yan Arewa mazauna Legas, kuma Shugaban ’Yan canji na Kasuwar Duniya ta Alaba, lhaji Adamu Marke ya ce al’ummar Arewa mazauna Kudu hankalinsu yana kwance ba sa dar-dar kan gabatowar zaben 2019. Alhaji Adamu Marke wanda kuma mai yin fashin baki kan al’amuran yau da kulum ne,ya bayyana haka ne a […]
Daya daga cikin shugabannin ’yan Arewa mazauna Legas, kuma Shugaban ’Yan canji na Kasuwar Duniya ta Alaba, lhaji Adamu Marke ya ce al’ummar Arewa mazauna Kudu hankalinsu yana kwance ba sa dar-dar kan gabatowar zaben 2019. Alhaji Adamu Marke wanda kuma mai yin fashin baki kan al’amuran yau da kulum ne,ya bayyana haka ne a zantawarsa da Aminiya, inda ya ce a wannan karon zaben ba ya tattare da batun kabilanci kamar yadda aka saba gani a baya, sannan ya ce a wannan karon babu maganar kaura da a baya wadansu ’yan Arewa mazauna Kudu kan yi idan lokacin zabe ya gabato. “Alhamdulillahi zaben badi ba zabe ne da ke kunshe da kabilanci ba, domin dukan manyan ’yan takarar Fulani ne, kuma dama can akwai aure a siyarar Arewa da Kudu maso Yamma. Arewa da Kudu maso Yamma a dunkule suke a siyasance don haka mu ba mu da wata fargaba. Fatarmu irin wannan ya dore a ci gaba da samun zaman lafiya da hadin kai,” inji shi.
Ya ce siyasar kabilanci da nuna wariyar addini ko bangaranci ba alhairi ba ce, “A irin wannan siyasa da muka gani a baya an samu matsaloli da dama a wancan lokaci. Da zarar lokacin zabe ya karato, za ka ga ana guje-guje, inda mutanen Arewa da ke zaune a Kudu suke komawa Arewa, haka na Kudu da ke Arewa su dawo gida amma a yanzu mun wuce wannan mataki mun samu ci gaba,” inji shi.
Alhaji Adamu Marke ya yaba wa kokarin gwamnati na tallafa wa kananan ’yan kasuwa da bashin jarin Naira dubu 10, inda ya ce kamata ya yi a fadada tsarin ta yadda matsakaita da manyan ’yan kasuwa za su amfana, “Koda yake mu ’yan canji ba bashi muke bukata ba, kowa ya san halin da kasuwar canji take ciki a yanzu. Al’amura sun tabarbare, tsare-tsaren gwamnati a wannan fannin sun sa kasuwancinmu ya tabarbare, fatarmu gwamnati ta yi tsare-tsaren da mu ma ’yan canji za mu amfana,” inji shi.