Ba ma goyon bayan Shugaban PDP ya yi murabus – Asabe Tirwun
Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP reshen Jihar Bauchi, Hajiya Asabe Isa Tirwun ta nuna damuwarta kan yadda wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar suka fara matsa lamba ga Shugaban Jam’iyyar ta kasa Ahmadu Adamu Mu’azu ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar. Hajiya Asabe ta bayyana haka ne lokacin da take zantawa da manema labarai a ofishinta […]
Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP reshen Jihar Bauchi, Hajiya Asabe Isa Tirwun ta nuna damuwarta kan yadda wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar suka fara matsa lamba ga Shugaban Jam’iyyar ta kasa Ahmadu Adamu Mu’azu ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar.
Hajiya Asabe ta bayyana haka ne lokacin da take zantawa da manema labarai a ofishinta da ke Bauchi, inda ta ce ta karanta a jaridu wani dan jam’iyyar, Alhaji Faruk B.B. Faruk ya kira taron manema labarai a Bauchi yana ba da shawara ga Shugaban Jam’iyyar da ya yi murabus a kashin kansa.
“Shawarar da ya bayar a gaskiya ba ta dace ba, domin kamata ya yi ya bada shawarwari kan yadda za a hada kan dukkan ’ya’yan jam’iyyar da suka fadi a zaben da aka gudanar a baya.
Ta ce masu kiran Alhaji Ahmadu Mu’azu ya yi murabus ba su da hujjar yin kiran domin shugaban y azo ne a daidai lokacin da take fama da rikici, kuma yana yin kokari wajen magance matsalolin jam’iyyar don haka bai dace a ce ya yi murabus ba, saboda babu wani laifi da ya aikata. “Ina kira da babbar murya ga ’ya’yan Jam’iyyar PDP su ci gaba da bada goyon bayansu ga Alhaji Adamu Mu’azu domin cikin kankanen lokaci PDP za ta sake farfadowa a sassan Arewa da Najeriya baki daya.