Ba ma nadamar ba Buratai sarautar Yarabawa – Masarautar Ibadan
Masarautar ta ce ta nada shi ne saboda jajircewarsa lokacin yana Hafsan Sojojin Kasa
Masarautar Ibadan da ke Jihar Oyo, ta ce sam ba ta nadamar ba tsohon Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), sarautar Aare Akinrogun na Ibadan.
Olubadan na Ibadan, Oba Lekan Balogun, ne ta bayyana hakan ranar Lahadi, lokacin da ya karbi bakuncin Buratai din a fadarsa, inda ya ce babu kuskure a ba shi sarautar.
- Shafin Instagram ya daina aiki a Rasha
- ‘Akwai yiwuwar ASUU ta zarce da yajin aikinta har sai abin da hali ya yi’
Tsohon Hafsan Sojojin, wanda kuma yanzu shi ne Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, dai ya jagoranci wata tawaga ne zuwa masarautar yayin ziyarar.
Da yake jawabi ta bakin dan uwansa, Sanata Kola Balogun, Olubadan din ya bayyana Buratai, wanda aka nada sarautar ta Aare Akinrogun lokacin yana rike da mukamin Hafsan Sojojin da cewa haziki ne kuma jajirtaccen soja, yana mai yi masa addu’ar ci gaba da samun karin daukaka.
Tun da farko dai Laftanar Janar Tukur Buratai ya bayyana nadin sabon Olubadan din a matsayin ajiye kwarya a burminta, saboda cancantarsa da rashin nuna banbanci.
Ya kuma taya mutanen masarautar murna kan nadin sabon basaraken, inda ya ce za su dara.
Daga cikin wadanda suka yi wa Buratai din rakiya yayin ziyarar akwai Birgediya Janar S.K. Usman (mai ritaya) da Laftanar Janar Lamidi Adeosun.
Ya kuma yi alkawarin kasancewa mai biyayya ga masarautar a matsayinsa na basarake a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.