Ba ma tsoro a sake fasalin Najeriya- Dattijan Arewa

Dattijan Arewa sun ce ko kadan Arewa ba ta tsoro a sake fasalin Najeriya. Wannan jawabin ya fito daga taron na Dattijan Arewan a lokacin da suke taro na musamman domin samar da matsaya a kan batun sake fasalin kasar a Kaduna. Taron wanda Cibiyar Bunkasa Binciken Yankin Arewa ta shirya, ya samu halartar manyan […]

Ba ma tsoro a sake fasalin Najeriya- Dattijan Arewa

Dattijan Arewa sun ce ko kadan Arewa ba ta tsoro a sake fasalin Najeriya.

Wannan jawabin ya fito daga taron na Dattijan Arewan a lokacin da suke taro na musamman domin samar da matsaya a kan batun sake fasalin kasar a Kaduna.

Taron wanda Cibiyar Bunkasa Binciken Yankin Arewa ta shirya, ya samu halartar manyan Arewa da suka haxa da ‘yan siyasa, malaman addinai, sarakuna da dai sauransu.

Da yawa daga cikin wadanda suka yi jawabi sun nuna damuwarsu kan yadda wasu bangarorin kasar suke nuna cewa Arewa na tsoro a sake fasalin kasar.

Gwamnan Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato, a jawabinsa ya ce “Maganar cewa wai Arewa na tsoro a sake fasalin Najeriya wai don muna karuwa da sauran sassan zuki ta malle ce kawai. Muna fada da babbar murya cewa ko kadan ba ma tsoro. A Arewa, muna maraba da batun sake fasalin kasar kamar sauran bangarorin qasar,” inji Tambuwal.

Shi ma a nasa jawabin, sakataren Majalisar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya nanata cewa Arewa ba ta tsoro a sake fasalin kasar. “Idan har ba za mu iya komawa kamar yadda muke a shekarar 1914 ba, to mu koma kamar yadda muke a  shekarar 1960, inda ake tsarin mulkin larduna. Arewa na so ta koma yadda take a da. Ko kadan Arewa ba ta tsoro,” inji Ango.