Ba mai iya tsorata mu da EFCC kan rikicin PDP – Lamido
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce sabon yankan rake a siyasa za a firgita ba irinsu da suka goge a fagen siyasa ba, inda ya ce babu wanda zai yi musu barazana da EFCC don su dainafadin gaskiya.Gwamna Lamido ya fadi haka ne a lokacin da ya amshi ’ya’yan Jam’iyyar PDP bangaren Garkuwa […]
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce sabon yankan rake a siyasa za a firgita ba irinsu da suka goge a fagen siyasa ba, inda ya ce babu wanda zai yi musu barazana da EFCC don su daina
fadin gaskiya.
Gwamna Lamido ya fadi haka ne a lokacin da ya amshi ’ya’yan Jam’iyyar PDP bangaren Garkuwa marasa jar hula a karkashin jagorancin Alhaji Sa’idu Dala suka ziyarce a makon jiya.
Gwamnan ya ce mutanen Kano mutane ne da suka san siyasar gaskiya da rashin tsoro kuma ba a yaudararsu ko a zo a ci su da mali.
Ya ce “Mu tsarinmu na siyasa dole ne a yi gaskiya domin haka marigayi Malam Aminu Kano ya gwada mana don haka yanzu ma dole mutane irinsu Bamanga su Jonathan su yi gaskiya muddin suna bukatar mu hada tafiya tare.”
Ya yaba wa al’ummar Jihar Bauchi kan fadin gaskiya cewa Bamanga ba dan goyo ba ne, “a baya kafin gaskiya ta bayyana mun yi mamakin jama’ar Bauchi na kin goya wa Bamanga Tukur baya, Bamanga ba ya da gaskiya kuma bai ci zabe ba, babu yadda za a yi agola ya zo gida ya shuka kabewa har ya rika neman fada da dan gida, inji shi.
Da yake mayar da jawabi Alhaji Sa’idu Dala ya ce su takaicinsu a Kano Jam’iyyar PDP ta mutu domin ba za yi wa sabon shugabannin jam’iyyar da Bamanga ya tura Jihar Kano biyayya ba, suna nan a bangaren Kawu Baraje ba Bamanga ba.
Ya ce kasancewar tsofaffin shugabannin jam’iyyar na jihar shugabancinsu ya kare kuma ba a yi sabon zabe ba shi ya sa suka ziyarci Gwamna Lamido inda akwai jagoranci na Jam’iyyar PDP domin su jaddada matsayinsu na magoya bayan bangaren Kawu Baraje.