Ba malamai kudi don goyon bayan Jonathan: Idan masu kagen ba su yi bayani ba sun cuci musulmi – Asadus Sunnah
Ustaz Musa Yusuf Asadus Sunnah na daya daga cikin malaman da sunansu ya bayyana a cikin wata takarda da ake cewa an ba su Naira dubu 500 zuwa miliyan daya domin tallar Shugaba Jonathan. Kuma yana cikin malaman da suka halarci taron da ofishin Mai ba Shugaba Jonathan shawara kan Harkokin Addinin Musulunci Masallacin Fadar […]

Ustaz Musa Yusuf Asadus Sunnah na daya daga cikin malaman da sunansu ya bayyana a cikin wata takarda da ake cewa an ba su Naira dubu 500 zuwa miliyan daya domin tallar Shugaba Jonathan. Kuma yana cikin malaman da suka halarci taron da ofishin Mai ba Shugaba Jonathan shawara kan Harkokin Addinin Musulunci Masallacin Fadar Shugaban kasa ya shirya a Kaduna da ake cewa an ba malaman Naira dubu biyar-biyar don mara wa Jonathan baya. A tattaunawarsa da wakilinmu ya ce batutuwan sharri ne da kage:
Aminiya: Kwanakin baya an gayyace ku taro a Dandalin Murtala da ke Kaduna, wane bayani za ka yi ga jama’a game da taron?
Asadus Sunnah: Bayanin shi ne baya ga batun zaman lafiya da taron ya kunsa akwai batutuwa biyu; fada wa shugabannin hakkokin da ke wuyansu da su al’umma kan nauyin shugabani da ke kansu. Domin yadda al’umma ke da hakki a kan shugabanni, shugabannin ma na da hakki a kansu. Wannan shi ne sakon da ni na isar a wurin taron .
Aminiya: Taron ya jawo cece-kuce inda wasu ke ganin kamar Jam’iyyar PDP ce ke neman amfani da malamai domin cimma muradinta, kuma ana zargin an ba ku kudi a wurin, me za ka ce?
Asadus Sunnah: Da farko mu ba yaran kowa ba ne, kuma babu wanda ya isa ya yi amfani da mu domin cimma wata manufa tasa. Na biyu korafe-korafen cewa an ba mu kudi, tun kafin a je taron mutane ke yada takarda cewa an ba mu kudi. Takardar na yawo a gari saboda haka ba za ka iya hana mutane fadin albarkacin bakinsu ba. Da kiyayya da soyayya kowannensu na da iyaka da shari’a ta ajiye. Sau da yawa idan mutane na kin abu, sukan ki shi fiye da ma’aunin da Allah Ya ajiye, haka idan suna son abu sukan so shi fiye da ma’aunin da Allah Ya aje masa.
Aminya: Wannan takarda me ta kunsa da haka da ya dame ku?
Asadus Sunnah: Wannan takarda ba damunmu ta yi ba, illa ta damu ‘yan uwa masoya da abokan arziki, domin duk mutumin da ke yin kira ga Addinin Allah akwai yiwuwar a kowane lokaci wani abu na kage zai iya samunsa, irin wannan a shirye muke cewa zai iya zuwa mana. ‘Yan uwa da abokan arziki suka damu a kan takardar har bukata ta taso aka yi taro aka ce ya kamata a kira taron ‘yan jarida. Wannan takarda tana yawo a gari cewa an ba mu kudi don tallar Shugaba Jonathan. Abin mamaki shi ne a Najeriya idan har Rabaran Mbaka zai iya fitowa ya yi Allah wadai da abin da ke faruwa a kasar nan, malaman Musulunci da su ya kamata a ce sun fi bayar da wannan sako amma a ce wai suna goyon bayan wannan abu, wannan kwarai da gaske yana da ban mamaki. Saboda haka wannan takarda ba mu da alaka da ita ba mu san ta ba. kage aka yi mana, sharri aka yi, kuma duk wadanda suka yi wannan takardar idan suna da dalilin da za su iya tabbatar wa duniya cewa (mun) karbi kudin kuma suka kasa fitowa su bayyana lallai sun cuci al’ummar Musulmi kuma Allah zai saka mata. Kuma mu da aka yi wa kage a wannan takarda in dai an zalunce mu an cutar da mu, kotun da Annabi Yusuf ya kai kara lokacin da aka ce ya yi zina, kotun da Nana A’isha ta kai kara lokacin da aka ce ta yi zina, mun kai kara wurin Mai wannan kotu. Mun kuma tabbatar Allah ba zai kyale ba, zai dauki mataki a kan abin da aka yi kusa ko nesa.
Aminiya: A cikin takardar an ce an ga inda kuka sa hannu cewa kun karbi kudin, haka ne?
Asadus Sunnah: A takardar babu sa hannun wani malami kuma yana daga cikin alamar ka karbi kudi a samu wuri da lokaci da rana da wanda ya bayar da wanda ya karba su saka hannu, duk babu wannan. Kuma ku ‘yan jarida ya kamata ku taimaka mana, Ambasada Gazali Tanko da aka sa sunansa a cikin takardar ku bin cika a tarihin Najeriya a cikin ambasadojin da aka yi a wadanda suka sauka da masu ci ko akwai mai wannan suna. Yana daya daga cikin binciken da za ku yi mana da kuma adireshin yanar gizon da suka bayar a bincika a gani tunda yanzu duniya a dunkule take, sai a gane ko da gaske akwai wannan adireshi da suka bayar.
Aminiya: Ko wannan takarda na da alaka da taron da kuka yi a filin Multala da wasu ke cewa na siyasa ne?
Asadus Sunnah: Takardar ba ta da alaka da taron, domin ta fito ne tun kafin a dage zabe. Sun so ne idan aka yi zabe sai su bar mu da rikici da jama’a, wato a yayin da ake rikicin zabe mu kuma muna rikici da jama’a. Da yake Allah ba azzalumin ba ne don mu samu damar kare kanmu sai aka dage zaben. Wannan taro kamar yadda aka gani wanda an sake saka shi a wani gidan talabijin mai zaman kansa a Kaduna, mu a matsayinmu na malaman addinin Musulunci akwai nauyin da Allah Ya dora mana akwai hakki a kan mabiya, akwai hakki na shugabanni kowa mu fada masa gaskiya. Na yi tunatarwa a wurin taron kuma abin da aka nemi in yi a wajen shi ne a fadi hakkin shugabani a kan mabiya da hakkin mabiya a kan shugabanni. Kuma na isar da sako kuma duk al’ummar da ta taru a wurin da karatun da aka yi sun tabbatar da mun isar wa al’umma sakon Allah kuma mun sauke nauyi. Wannan taro ba ya da alaka da siyasa kwata-kwata na kusa ko na nesa.
Aminiya: A wajen taron akwai bayanin cewa wai kun bi layi wajen amsar kudi, me za ka ce?
Asadus Sunnah: Akwai wanda ya je wurin ya dauko karatun ya sa a talabijin, wannan layi na karin kumallon safe ne da aka bayar a wurin. Domin dabi’ar ’yan Najeriya mafi yawancin idan ba sa’a ba, ko ruwan leda za ka raba sai an yi wawarso. Saboda su karbi abincin cikin tsari sai aka ce a yi layi. Ba kuma duk wanda ya je wurin ba ne malami, sama da mutum 3,500 ne suka halarci taron. Akwai jama’ar gari wadanda suka halarci taron a matsayin masu saurare su ne aka ba kudin mota domin komawa inda suka fito. Ni na je amma ba a ba ni kudi ba, kamar yadda wasu ke cewa wai ina saukowa aka ba ni Naira miliyan 20, wasu ma cewa suka yi wai sun ga lokacin da ake jejjera kudin a motata, wanda wannan abu ne da hankali ba zai iya dauka ba. Cewa an ba ka kudi a gaban jama’a kuma har kana jerawa a cikin mota, wannan ba gaskiya ba ne.
Aminiya: Su wa kuke zargi da yi muku wannan kage?
Asadus Sunnah: Muna da makiya da yawa akwai wadanda muke da bambancin akida da su, akwai wadanda da dama mun samu matsalar da su, akwai ‘yan siyasa da muka samu matsala da su. Saboda haka kowa muna da tuhuma a kansa, sai dai wanda ya kubbuta kawai. Amma yanzu babu wani mutum takamaimai da muka ayyana muka ce shi muke tuhuma domin tuhumarmu tana iya fadawa a kan duk wanda muka san muna gaba da shi.
Aminiya: Mene ne sakonka ga jama’a?
Asadus Sunnah: Sakona ga jama’a shi ne su ji tsoron Allah, mumini yana bada uzuri yana kuma kyautata zato, munafuki ne ba ya bada uzuri kuma ba ya kyautata zato. Don haka a kyautata zato a kuma bada uzuri.