Ba marabar Buhari da Abacha – Obasanjo
Obasanjo na bukatar likita ya duba lafiyarsa – Buhari Takaddama ta sake kaurewa a tsakanin tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo da Shugaba Muhammadu Buhari, bayan da Obasanjo ya ce mulkin Buhari bai da maraba da na Abacha saboda yadda Shugaban ke son ya lashe zabe ko ta halin kaka. Obasanjo ya fadi haka […]
- Obasanjo na bukatar likita ya duba lafiyarsa – Buhari
Takaddama ta sake kaurewa a tsakanin tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo da Shugaba Muhammadu Buhari, bayan da Obasanjo ya ce mulkin Buhari bai da maraba da na Abacha saboda yadda Shugaban ke son ya lashe zabe ko ta halin kaka.
Obasanjo ya fadi haka ne a wata wasika da ya rubuta mai taken “Damuwa da kuma mataki,” inda ya zargi Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), cewa ta shirya yin magudi a zaben na bana. A cikin wasikar wadda ita ce ta biyu da Obasanjo ya soki Buhari, ya bayyana Hukumar INEC da wani bangare na Jam’iyyar APC, tare da bayyana cewa APC na yin katsalandan ga harakokinta.
Obasanjo ya yi misali da zaben Jihar Osun da INEC ta ce ba a kammala ba, “Hakan ya tabbatar da INEC tana iya sanar da jam’iyyar da take so ta ci zabe ko da kuwa ta sha kaye ko kuma akwai matsaloli da za su iya sa a soke zaben ko ta ce sai an je zagaye na biyu,” inji shi.
Sai ya yi kira ga ’yan Najeriya su tashi tsaye a yaki gwamnatin Buhari kamar yadda aka yaki ta Abacha ta hanyar yin addu’o’i a masllatai da coci-coci.
Obasanjo na bukatar likita ya duba lafiyarsa – Buhari
A martanin da gwamnati ta mayar kan wasikar ta Cif Olusegun Obasanjo, Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu, ya bayyana wasikar a matsayin wani yunkuri na wadansu ’yan siyasar da suka gaza ja da Shugaba Buhari a siyasance suka koma cin dunduniyarsa.
Gwamnatin ta ce ga alama Cif Obasanjo yana bukatar kwararren likita ya duba lafiyarsa, inda ta yi masa fatan samun lafiya cikin gaggawa. “Shawara a gare shi, shi ne ya nemi likita, ya nemi magani. Muna yi masa fatan Allah Ya ba shi lafiya,” inji sanarwar.
Gwamnatin ta kuma bayyana Obasanjo da mutum mai hassada saboda ya san Shugaba Buhari ya fi shi martaba a idon duniya. Ta ce Cif Obasanjo yana juya wa duk mutumin da ya ga ba zai kyale shi ya yi abin da ya so ba, kuma ya fitar da wasikarsa tasa ce domin ya rasa mafita ta ci gaba da tatsar haramtacciyar dukiyar da ya saba yi a shekarun baya.
Kakakin Shugaban Kasar ya ce zaben Shugaban Kasa da za a yi a watan gobe zai kasance sahihi kamar yadda Shugaba Buhari ya yi alkarwari ga kasar nan da duniya baki daya.
Kakakin Shugaban ya ce, “Abin da muke so mu nuna musu shi ne, kayen da suka sha a wancan karon somin tabi ne, kuma wanda za su gani a zabe mai zuwa sai ya rugurguza su a siyasance. Daga wannan lokacin ba za a sake jin kansu ba, domin karshen siyasarsu ya zo. Jama’a za su kada kuri’a kuma za su yi musu kayen da ba su taba tsammanin zai same su ba.”
Sanarwar ta bayyana Cif Obasanjo da babban matsoraci, inda ta zarge shi da karkatar da Dala biliyan 16, kudin da ta ce an ware domin samar da wutar lantarki a lokacin mulkinsa, aikin da ta ce ba a yi ba, don haka ta ce yana cike da tsoron ranar da za a tuhume shi ya bayyana abin da ya yi da kudaden.
A kan batun yaki da kungiyar Boko Haram kuwa, Malam Garba Shehu ya yi watsi da ikirarin Cif Obasanjo cewa gwamnatin Buhari na da hannu wajen fadawar da Libya ta yi cikin rikici. Garba Shehu ya ce “Ka dubi Najeriya, ka ce wai Boko Haram a karkashin mulkin Shugaba Buhari ta fi karfi, wannan magana ce ta mafarki.Ko kuma ka zargi Shugaba Buhari don kasar Libya ta rushe… ai a lokacin gwamnatinsu ta PDP ce ke mulki, wane mataki suka dauka a kai?” Sanarwar ta yi watsi da wasikar ta Cif Oasanjo musamman inda ya ce Shugaba Buhari ya shirya murde zaben Shugaban Kasa da zai gudana kasa da mako hudu masu zuwa.
Garba Shehu ya ce abin takaici ne a ce dan shekara 90 da haihuwa ya zama “tsohon makaryaci,” kuma Shugaba Buhari zai ba marada kunya.
Duk Abin da Abacha da Buhari suka yi Obasanjo ya yi fiye da shi – Balarabe Musa
Daga Mohammed Yaba, Kaduna
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Balarabe Musa ya maida wa tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo martani a kan suka tare da danganta salon Gwamnatin Muhammadu Buhari da ta marigayi Janar Sani Abacha inda ya ce duk abin da ya soki Buhari da Abacha da shi, Obasanjon ya yi fiye da hakan a lokacin mulkinsa.
Balarabe Musa ya ce bai kamata mai hankali ya yarda da maganganun na Obasanjo bam inda ya ce babbar matsalar Obasanjo ita ce dauka yake ya fi kowa a kasar nan. Alhaji Balarabe Musa ya bayyana haka ne a zantawarsa da Aminiya a Kaduna kan kalaman na Obasanjo.
“Mene ne Abacha ya yi da shi bai yi fiye da hakan ba, wato Obasanjo da kansa ke nan. Idan har akwai shaida a kan abin da ya ce Abacha ya yi shi ai ya yi fiye da hakan. To, mun gaji da cewa Abacha ya yi kaza ko bai yi kaza ba, domin ba kuma muna cewa Abacha ya aikata ko bai aikata ba ne, amma su masu zarginsa sun aikata fiye da abin da shi Abachan ya aikata. Koma me Abacha ya yi ba zargin satar kudi ba, to shi an kwato daga wajensa su kuma sun sace. In kuma maganar cewa Abacha ya daure mutane to shi Obasanjo ba ya yi fiye da haka ba? Ba dan uwansa Bayarabe Minista Bola Ige aka kashe ba amma Obasanjo bai yi komai a kai ba. Maimakon haka ma wanda ake zargin cewa yana da hannu a kashe Bola Igen yana cikin kurkuku aka ce wai ya ci zabe ba ya zama Sanata?,” ya yi tambaya.
Balarabe Musa ya ce, “Magana ta biyu ai Abacha ya fi Buhari inganci wajen shugabanci, dalili shi ne Abacha ba yaron kowa ba ne a shugabanci. Wa ya taba maganar cewa Abacha yaron wani ko akwai wadansu da ke juya mulkinsa? Babu wanda ya yi wannan zargi kowa ya dauka in ma laifi ne shi ya yi. Wannan (Buhari) kuma cewa ake wadansu ke tafiyar da mulkin ba shi ba. Saboda haka Obasanjo mutane su gane cewa fa shi gani yake duk a duniyar nan babu wani gwani sai shi. Dalili shi ne tun lokacin da ya mika mulki yana Shugaban Kasa na soja duk wanda ya zo bayansa koda ya goyi bayan zuwansa daga baya sai ya soke shi kuma ya hada waya domin a ki jinin mutumin kuma karshensa gwamnatinsa ta fadi. Sana’ar Obasanjo ke nan kuma har yanzu bai daina ba. Wai shin ba Obasanjo da kansa ya tashi ya ce shi yana goyon bayan Buhari ba kuma da shi aka yi komai a lokacin yakin neman zabe har Buhari ya ci zabe.”
“Sai ga shi kuma yanzu yana yi wa Buharin abin da ya yiwa sauran. Obasanjo din nan duk da suna tare da Atiku kuma duk da barna da suka yi a mulki tare suka yi, har ta kai ga ma a lokacin da Atiku ke Mataimakin Obasanjo suna dasawa zan ba ka misali a lokacin zaben fid da gwani a wancan lokaci ko na Jam’iyyar PDP ko a wata jam’iyya wajen Atiku ake zuwa, saboda damar da Obasanjo ya bai wa Atiku. Ni zan iya fada maka gwamnoni biyu da na sani daya a kasar Yarbawa daya kuma a nan arewa wadanda suka zama Gwamna ba dao komai ba sai don saboda Atiku ya tsaya masu lokacin yana Mataimakin Obasanjo, amma daga baya yaya ta kwashe a tsakaninsu da Atiku? To haka obasanjo yake,” inji shi.
Abin da ya sa Obasanjo ke fada da shugabannin da suka biyo bayansa – Tanko Yakasai
Daga Lubabatu I. Garba, Kano
Daya daga cikin dattawan Arewa Alhaji Tanko Yakasai ya ce ba wani abu ne ya sa tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ke fada da shugabbannin da suka gaje shi ba, illa kawai yana kwatanta al’adar soja.
Alhaji Tanko Yakasai ya ce kasancewar soja suna karbar mulki ne bayan sun tunbuke gwamnatocin da ke gabansu shi ya janyo suke kafa wa shugabannin da suka gada ko suka biyo bayansu kahon zuka. “Idan kin duba dukan sojojin da suka yi mulki kasar nan sun karbi mulki ne ta hanyar juyin mulki idan ban da Shugaban Kasa Janar Gowon. Don haka da zarar sun hau kujerar mulki sai ka ga suna gaba da wadanda suka gada, wannan kuwa ya faro tun daga kan mulkin Janar Murtala har zuwa kan Babangida,” inji shi
Alhaji Tanko Yakasai ya ce wani abu da ke sanya shugabannin soja zagin junansu shi ne rashin manufa. “Kin ga a lokacin dukan siyasa da aka yi a baya za ki ga kowace jam’iyya tana da manufa ma’ana tana da wani abu da take son cimmawa. su kuwa soja ba su da wata manufa guda da suka tsara za su bi wajen gudanar da mulkinsu. A wancan lokaci shugabanni da yake suna yin siyasa da gaskiya ba su zagin junansu sai da su zagi manufofin junansu. Misali a Jamhuriyya ta Farko tsarin NEPU na da manufar ceton talakawa sai kuma NPC da ke da manufar kyautata sha’anin noma, haka abin ya gangaro har kan jam’iyyun NPN da PRP da sauransu. Kuma a wancan lokacin idan kin duba yawanci a wakoki ake yin habaici da zambo da sauransu, amma lokacin da soja suka karbi mulki sai suka fara zagin junansu saboda ba su da manufar da za su zaga. Lokacin da Buhari ya hau sai ya fara zagin Shagari haka abin ya ci gaba har zuwa yau.” Inji shi.
Tanko Yakasai ya ce “Obasanjo ya kwatanta Buhari da Abacha ne saboda dukansu sojoji ne da suka yi mulkin kasa ba tare da wata manufa ba sai mulkin kama-karya. Ba su damu da tunanin hadin kai da talakawa ba.”
Lokacin da Obasanjo ya fara sukar shugabanni
Shehu Shagari
Shugaba na farko da Obasanjo ya yi wa irin wannan wasika shi ne Alhaji Shehu Shagari wanda ya yi mulki Najeriya daga 1 ga Oktoba 1979 zuwa 31 ga Disamban 1983.
’Yan watanni da hawansa mulki a wa’adi na biyu a 1983, Obasanjo ya yi suka ga Shehu Shagari kan tabarbarewar tattalin arziki inda ya ce hakan ya jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali. Kuma yi yi korafin cewa cin hanci da rashawa sun yi katutu a gwamnatinsa.
Makonni kadan da wannan suka ce sojoji suka yi wa Shagari juyin mulki a karshen 1983.
Janar Ibrahim Babangida
Bayan da Janar Babngida ya kaddamar da shirin sake fasalin tattalin arziki na kowa ya ji a jikinsa (SAP) wanda ya kara radadin talauci da wahalar da talakawa ke fuskanta a kasar nan, sai Obasanjo ya ari bakin talakawa ya ci masu albasa inda ya soki mataki na gwamnatin Babangida.Kuma bayan soke zaben 12 ga Yunin 1993 da ake cewa Cif MKO Abiola ya lashe, Obasanjo ya ci gaba da sukar gwamnatin Babangida har ya sauka daga mulki ran 27 ga Agustan 1993.
Janar Sani Abacha
Obasanjo bai tsallake gwamnatin Janar Janar Sani Abacha ba, inda ya taba bayyana gwamnatin a matsayin marar alkibla. Haka a wata hira da ya yi da BBC a lokacin, ya zargi gwamnatin Abacha da almubazzaranci da albarkatun kasa.
Umaru Musa ’Yar’aduwa
Takun sakar da ta auku a tsakanin ’Yar’aduwa da Obasanjo ta bayyana ce sakamakon rashin gamsuwar da Obasanjo ya yi da mulkin ’Yar’aduwa. Obasanjo ya rubuta wa gwamnatin ’Yar’aduwa wasika tun a farkon mulkinsa, inda ya ce lallai ne shugaban ya zage dantse a yadda yake tafiyar da ayyukansa. Wasikar ta karfafa rashin jituwa a tsakanin Obasanjo da magajinsa.
Lokacin da ’Yar’aduwa ya tafi Saudiyya jinya ba tare da ya mika mulki ga mataimakinsa ba, inda aka yi ta cece-ku-ce, Obasanjo da wadansu shugabanni sun ziyarci ’Yar’aduwa a Saudiyya. Kuma dawowar Obasanjo ke da wuya, ya bayyana bukatar a fara neman wanda zai gaje shi.
Goodluck Jonathan
Ranar 2 ga watan Disamban 2013, Obasanjo ya rubuta budaddiyar wasika ga Shugaba Goodluck Jonathan mai taken “Kafn lokaci ya kure,” inda a ciki Obasanjo ya ce ya rubuta budaddiyar wasikar ce saboda a baya ya rubuta wa Jonathan wasiku hudu cikin sirri bai ba shi amsa ba. Ya ce ya zama dole ya rubuta wasikar ce saboda ya ga alamun gwamnatin Jonathan tana da kamanni da gwamnatin Abacha, inda ya yi kira ga Jonathan ya dage wajen ganin Najeriya ba ta rabu ba a tsakanin Musulmi da Kiristoci ko Kudu da Arewa. Jonathan ya ba wasikar amsa inda ya musanta duk wani bayani da Obasanjo ya yi.
A watan Yunin bara, Obasanjo ya yi kukan cewa Buhari yana hada shaidun bogi domin ya kama shi don tsare shi dindindin.
Wasikar da Obasanjo ya rubuta ga Shugaba Buhari, bai boye maitarsa ba, ta ganin ya yi duk mai yiwuwa don ganin Buhari bai koma mulki a bana ba.