Ba matasa ragamar mulki ba shi ne mafita ba – Shugaban kungiyar CPP
An bayyana cewa bai wa matasa ragamar mulki ba shi ne mafita ga halin da kasar ta tsinci kan a a ciki ba, bilhasali ma hakan sai dai ya dada jefa kasar cikin wata matsalar ta daban. Sakataren kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) na Kudancin Jihar Kaduna, Alhaji Iliyasu Musa ne ya bayyana haka yayin […]

An bayyana cewa bai wa matasa ragamar mulki ba shi ne mafita ga halin da kasar ta tsinci kan a a ciki ba, bilhasali ma hakan sai dai ya dada jefa kasar cikin wata matsalar ta daban.
Sakataren kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) na Kudancin Jihar Kaduna, Alhaji Iliyasu Musa ne ya bayyana haka yayin tattaunawarsa da Aminiya a makon jiya.
Alhaji Iliyasu ya ce akwai matukar hadari ga mutumin da bai gama mallakar hankalinsa ba a ce za a dauki mulkin jama’a a damka masa.
Sakataren, ya ce yadda siyasar kasar nan take ta siyasar ubangida, ko da an bai wa matasa mulkin kasar, to wadansu tsofaffin da aka guje mawa dole su za su rika juya akalar matasan ta bayan fage. “Babu wani matashi da zai fito neman wani matsayi ko mukami face ya bukaci wani babba da zai tsaya masa wajen dawainiyar kashe-kashen kudin zirga-zirga neman kuri’a da sauransu don haka a ganina ko da an bai wa matasa ragamar shugabanci zai zama canjin salo ne kawai na ci gaban mulkin tsofaffin da aka guje mawa domin kowa zai cusa nasa ne,” inji shi.
Da ya juyo kan salon da wadansu daga cikin sarakunan yankin Kudancin Kaduna ke yi na bai wa matasa ragamar yin magana da yawunsu tattare da cewa akwai sarakuna da dattawa da kuma malamai amma sai su nuna wani su ce shi ne shugaban matasa don haka shi zai yi magana a madadinsu da sauran jama’ar gari gaba daya, ya ce hakan zubar da kimar sarauta ce da nuna dattawansu ba a bakin komai suke ba. Ya ce, idan har ba za su iya tsawatarwa da kuma yin magana a madadin jama’arsu ba, to kamata ya yi wadannan sarakuna su tube rawunnansu su nada wa matasan.
Alhaji Iliyasu, wanda har ila yau shi ne Shugaban kungiyar Wanzar da Zaman Lafiya ta Community Peace Partnership (CPP) ta karamar Hukumar Jama’a ya ce in sarakunan za su yi mulki tsakaninsu da Allah to Ya kamata su taimaka wa gwamnati ne wajen kokarin samar da zaman lafiya.