…Ba maulidi muka je Fadar Shugaban Kasa ba –Ahmad Sulaiman

A daidai lokacin da ake bikin maulidin bana ne aka ga taron malaman Izala da Darika a Fadar Shugaban Kasa, lamarin da ya jawo cece-ku-ce, har wadansu ke cewa malaman Izala sun je taron maulidi. Aminiya ta zanta da Alaramma Ahmad Sulaiman, daya daga cikin malaman Izala da suka halarci taron addu’ar, inda ya bayyana […]

…Ba maulidi muka je Fadar Shugaban Kasa ba –Ahmad Sulaiman

Sheikh Ahmad Sulaiman riqe da abin magana lokacin da suke karva-karva wajen addu’a a Fadar Shugaban Qasa

A daidai lokacin da ake bikin maulidin bana ne aka ga taron malaman Izala da Darika a Fadar Shugaban Kasa, lamarin da ya jawo cece-ku-ce, har wadansu ke cewa malaman Izala sun je taron maulidi. Aminiya ta zanta da Alaramma Ahmad Sulaiman, daya daga cikin malaman Izala da suka halarci taron addu’ar, inda ya bayyana matsayarsu a kan lamarin:

 

Wane  taro ne kuka je a Fadar Shugaban Kasa?

Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya bugo mini waya ina Kano, ya bukaci ni da Dokta Sulaiman Kumo cewa mu wakilci kungiya a wajen taron, kasancewar shi da Sakatare Sheikh Kabiru Gombe ba sa kasar nan. Sai dai maganar gaskiya babu batun maulidi a lamarin kamar yadda gayyatar ta nuna da kuma abin da ya gabata a wajen taron. Taro ne da aka shirya don yi wa kasa addu’a musamman a kan matsalolin tsaro da kuma fadakarwa a kan harkar miyagun kwayoyi da tarbiyya da kuma aikin yi. Sai dai kasancewar taron ya hada masu akida daban-daban kamar masu yin maulidi, kuma ga shi a cikin watan ake, sai wani ya yi amfani da wannan dama ya ce ana taron ne a matsayin maulidi. Sai dai nan take wani ya yi masa raddi inda ya sanar da cewa mu ba a kan maulidi aka gayyato mu ba. An gayyace mu ne a matsayin taro na yi wa kasa addu’a da fadakarwa a kan abubuwa.  Wani abin kuma da na kula da shi, shi ne  gidan Talabijin na Kasa (NTA) da ya dauko labarin, ya alkanta taron da maulidi, sabanin abin da aka rubuta a taken taron da abin da a ka gabatar a wajen. Akwai malumanmu na Ahlussunah da dama da suka halarci taron kamar Sheikh Abdulwahab Abdallah Limamin Ahlus Sunnah Wal Jama’a da Dokta Abdallah Gadon Kaya da Dokta Lawan Abubakar da Sheikh Muhammad Bin Usman. Sannan daga bangaren Darika akwai Malam Shehu Shehi na Tijjaniyya da Bazallah na Kadiriyya da  wadansu malumansu da yawa. Duk an gabatar da lacca a kan wadannan darussa da aka ware, sannan a karshe aka kebe wadansu daga cikinmu suka gabatar da addu’a.

Shin me ya sa Izala ba ta yin mauldi, har wadansu na bayyana hakan a matsayin rashin kaunarsu ga Manzon Allah?

Duk da dai ka san ni ba cikakken malami ba ne, sai dai abu guda da zan kawo a nan shi ne: Shin a dukkan littafanmu na addini da aka sani wadannda mu da su duk mu na karanta su, kama daga Kawa’idi zuwa Risala har ya dangana da Mudawwana, a bangaren Hadisi kama daga Muwadda Maliki da su Buhari, idan dai wannan maulidi da ake yi addini ne, shin me ya sa ba a kawo shi a cikin wadannan littatafan ba. Shin girmansa ne ya sa ya fi karfin a kawo shi, ko dai rashin asalinsa ne. Ko dai duk wadanda suka yi littatatafan nan ba su san da shi ba ne a addini? Bayan nan duk wanda ke son Manzon Allah (SAW) ai a bayan matarsa Sayyidatuna A’isha (RA) yake, ko kuma mahaifinta Sayyidina Abubakar (Allah Ya yarda da shi). To da shi da sauran sahabban nan uku wato Umar da Usman da Aliyu (Allah Ya yarda da su), wadanda Annabi (SAW) ya ce mu karbi shiriyarmu daga wajensu, duk babu wanda ya yi maulidin nan a cikinsu. Idan da’awar so ake yi, shin mun fi su sonsa ne? Ashe ke nan wannan abin ba addini ba ne, bidi’a ce, mu kuma Izala aikinmu dama shi ne, mun kafa kungiyar ce don yakar bidi’a da kuma raya Sunnah, gwargwadon iyawarmu.