Ba Mu Ƙara Kuɗin Mota Ba —RTEAN

Duk da haka an yi ƙarin Naira dubu ɗaya a kuɗin motar zuwa Kano

Ba Mu Ƙara Kuɗin Mota Ba —RTEAN

Wata tashar mota

Ƙungiyar Direbobi ya RTEAN ta yi iƙirarin cewa ƙarin kuɗin man fetur bai sa sun ƙara kuɗin mota a tasharsu ba a Jihar Gombe.

Shugaban Kungiyar RTEAN a Jihar Gombe, Musa Muhammad Gidado, ya bayyana cewa ba su ƙara kuɗin mota zuwa Kaduna ba daga Naira 18,000.

Hakazalika kudin mota zuwa Filato ma Naira 7,000 ne, shi ma ba’a ƙara ba.

A cewarsa, a tasharsu ta RTEAN, wannan karin farashin man fetur bai sa sun kara kudin mota ba, in banda Naira 1000 da aka ƙara a kuɗin motar Kano.

Wasu fasinjoji da suka zanta da wakilinmu sun bayyana cewa gaskiya ƙarin kudin mai zai hana mutane yin tafiye-tafiye saboda rayuwar ta ƙara tsada fiye da da.

Wani mai suna Adamu Danjuma ya ce yana roƙon Shugaban Kasa, Bola Tinubu, da ya dawo da tallafin man fetur, in ba haka ba tafiya za ta gagari masu ƙaramin karfi.

A bangaren ’yan Keke NAPEP kuwa, fasinjojin da muka zanta da su sun bayyana cewa inda suke biyan Naira 100 a baya, yanzu an ƙara zuwa Naira 150 ko N200.

Sun shaida wa wakilin namu cewa hakan zai iya hana su zuwa unguwa, musamman mata da ke zuwa asibiti ko gidan biki.

Wakikinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin shugabannin ƙungiyar ’yan Keke NAPEP don jin halin da ake ciki.

Ya je ofishin ƙungiyar bai sami shugabannin ba, amma wani da aka samu a wajen ya ce ba su yi wani taro ba a kan lamarin.

Amma ya ce kowannensu ya ƙara farashi yadda zai iya samu ya mayar da kuɗin mansa saya saboda yadda suke sayen man fetur a gidajen Mai an ƙara kuɗi.

Dalilin da ba zan bai wa Gwamnatin Tinubu shawara ba — Sarki Sanusi

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana