‘Ba mu amince a kara wa Sheriff wa’adin shugabancin PDP ba’

kungiyar Yada Manufofin Jam’iyyar PDP ta kasa, Reshen Jihar Filato ta kalubalancin shugabannin Jam’iyyar PDP na yankin Kudu maso Yamma kan kiran da suka yi na a kara wa’adin shugabancin Sanata Ali Modu Sheriff zuwa shekarar 2019.Shugaban kungiyar Chung Solomon Baba ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Jos a […]

‘Ba mu amince a kara wa Sheriff wa’adin shugabancin PDP ba’
‘Ba mu amince a kara wa Sheriff wa’adin shugabancin PDP ba’

kungiyar Yada Manufofin Jam’iyyar PDP ta kasa, Reshen Jihar Filato ta kalubalancin shugabannin Jam’iyyar PDP na yankin Kudu maso Yamma kan kiran da suka yi na a kara wa’adin shugabancin Sanata Ali Modu Sheriff zuwa shekarar 2019.
Shugaban kungiyar Chung Solomon Baba ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Jos a ranar Litinin.
A ranar Asabar da ta gabata ne wata sanarwa dauke da sa hannun Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose da takwaransa na Jihar Ondo Olusegun Mimiko da Cif Olabode George da wadansu jiga-jigan jam’iyyar uku, ta ce Jam’iyyar PDP da ke Kudu maso Yamma ta amince shugabancin jam’iyyar na kasa ya kasance a Arewa, don kada a rika ganin kamar jam’iyyar ta wani yanki ne, sannan a bar Sanata Sheriff ya ci gaba da juya akalar jam’iyyar har zuwa 2019.
Chung Baba ya ce “Mun yarda da cewa a bar shugabancin jam’iyya na kasa a yankin Arewa don kada a rika ganin jam’iyyarmu kamar ta yanki guda ce, wannan ya yi daidai. Amma su bayyana sunan mutum daya daga Arewa, sannan su ce a ba shi shugabancin jam’iyya, to wannan ne ba mu amince ba. Har kambama shi suka wai mutum ne mai yakana da burin aikata alheri. Idan har da suna son jam’iyyar nan a zuciyarsu, to sai su yi shiru, domin su bar Arewa ta fitar da wanda zai shugabancin jam’iyyarmu. A Arewa muna da wadanda suka fi Sheriff, wadanda za su farfado da jam’iyyar nan, sannan su daga darajarta a idon duniya.”
Mista Baba ya kara da cewa barin Sanata Sheriff a matsayin shugaban Jam’iyyar PDP har zuwa 2019 ba zai haifar wa jam’iyyar da mai ido ba, domin mutane da yawa a Arewa suna ganin yana da bakin fenti sakamakon rikicin Boko Haram.