Ba mu amince da hadakar kamfanin simintin Ashaka da WAPCO ba – Al’ummar Funakaye

Al’ummar karamar Hukumar Funakaye a Jihar Gombe sun nuna rashin amincewa da niyyar kamfanin siminti na Ashaka na yin hadaka da kamfanin WAPCO daga Kudancin kasar nan.Al’ummar Funakaye sun bayyana rashin amincewar ce ta bakin shugabansu Dokta Garba Muhammad Bajoga (Karzai) a lokacin da suka ziyarci cibiyar ’yan jarida ta Gombe don nuna rashin yarda […]

Ba mu amince da hadakar kamfanin simintin Ashaka da WAPCO ba – Al’ummar Funakaye
Ba mu amince da hadakar kamfanin simintin Ashaka da WAPCO ba – Al’ummar Funakaye

 Dakta Garba Muhammad BajogaAl’ummar karamar Hukumar Funakaye a Jihar Gombe sun nuna rashin amincewa da niyyar kamfanin siminti na Ashaka na yin hadaka da kamfanin WAPCO daga Kudancin kasar nan.
Al’ummar Funakaye sun bayyana rashin amincewar ce ta bakin shugabansu Dokta Garba Muhammad Bajoga (Karzai) a lokacin da suka ziyarci cibiyar ’yan jarida ta Gombe don nuna rashin yarda da hadakar.
Dokta Garba Bajoga, ya ce tunda aka kafa kamfanin siminti na Ashaka shekara 35 da suka wuce riba yake samu ba faduwa ba, shi kuwa kamfanin WAPCO fiye da shekara biyar bai samu koda kwandala a matsayin riba ba.
Ya ce a duk fadin kasar nan an san kamfanin siminiti na Ashaka, wanda saboda ingancinsa ake yi masa lakabi da Tauraron Arewa, kuma duk wani aikin gada ko na kwalbati da shi ake yi, “amma sai ga shi ana son a yaudari ’yan kasuwar siminti na Funakaye to ba za mu yarda ba,” inji Karzai.
Dokta Bajoga, ya ce kasuwanci don riba ake yin sa in kuwa haka ne don me za a ce za a yi hadaka da kamfanin da shekara fiye da biyar bai samu ribar ko kwandala ba.
Ya ce saboda ribar da kamfanin yake samu ne ya sa a kwanakin baya aka yi bikin fadada yawan simintin da zai rika samarwa a shekara, ya ce idan hadaka za a yi to a samu kamfanin da ya cancanta ba WAPCO ba.
Daga nan sai ya ce a matsayinsu na al’ummar garin Funakaye inda nan ne kamfanin yake za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin ba su bari wannan hadaka ta yiwu ba.