Ba mu amince da takarar Jonathan ba – Lamido

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya yi fatali da matakin da aka ce gwamnonin jam’iyyarsata PDP sun dauka a lokacin taron jam’iyyar na shiyya a Kaduna, inda aka ce sun amince su mara wa Shugaba Goodluck Jonathan a zaben badi.Gwamna Lamido ya bayyana haka ne ta bakin Mataimakinsa Alhaji Ahmed Mahmud Gumel a wani […]

Ba mu amince da takarar Jonathan ba – Lamido
Ba mu amince da takarar Jonathan ba – Lamido

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya yi fatali da matakin da aka ce gwamnonin jam’iyyarsa
ta PDP sun dauka a lokacin taron jam’iyyar na shiyya a Kaduna, inda aka ce sun amince su mara wa Shugaba Goodluck Jonathan a zaben badi.
Gwamna Lamido ya bayyana haka ne ta bakin Mataimakinsa Alhaji Ahmed Mahmud Gumel a wani taron manema labarai da ya kira a Dutse.
Gwamnan ya ce an rubuta wannan takarda ta amincewa da mara wa Shugaba Jonathan baya ne tun kafin a gudanar da taron gwamnonin wanda hakan ya saba wa qa’ida da tsarin dimkoradiyya.
Gwamna Lamido ya ce amma suna biyayya ga uwar jam’iyyarsu ta PDP sai dai matakin da gwamnonin suka dauka na qoqarin qaqaba Shugaba Jonathan a matsayin dan takarar Shugaban Qasa a 2015 ba su amince da shi ba.
Ya ce sun dauki matakin haka ne saboda gazawar gwamnatin Jonathan na cika wa Jihar Jigawa alqawurran da ta dauka a lokacin yaqin neman zaben baya.
Taron wanda aka gudanar da shi a Kaduna ranar Lahadi gwamnonin jihohin Katsina Barista Ibrahim Shema da takwararsa na Jigawa Alhaji Sule Lamido sun qaurace masa, inda gwamnonin Kaduna da Kebbi ne kawai suka halarce shi.
Rahotanni sun nuna cewa taron dai an shirya shi ne da nufin yin kira ga Shugaba Jonathan ya tsaya takara a zaben 2015. Sai dai a yayin da aka fara taron sai wasu ’ya’yan jam’iyyar wadanda manufar taron bai yi musu dadi ba suka fara ficewa daga dakin taron domin nuna adawarsu.
Manyan ’yan Jam’iyyar PDP ciki har da shugaban jam’iyyar na qasa Alhaji Ahmadu Adamu Ma’azu da Mataimakin Shugaban Qasa, Alhaji Namadi Sambo da wasu jiga-jigan jam’iyyar a Arewa maso Yamma ne suka halarce shi.
Sai dai babu wanda ya fadi dalilin rashin halartar Gwamna Lamido da Gwamna Shema, amma wata majiya ta ce hakan na da alaqa ne da sha’awar tsayawa takarar shugabancin qasa da Sule Lamido ke da shi a yayin da shi kuma Shema ke sha’awar a tsayar da shi Mataimakin Jonathan a zaben 2015.
Daga cikin mutanen da suka fice daga dakin taron domin nuna adawarsu sun hada da jagoransu wani dan Majalisar Jihar Katsina wanda ya qi fadin sunansa.
Ya ce “Babu wanda ya fada mana cewa taro ne na goyon bayan Shugaba Jonathan ko wani dan takara. An dai kira mu ne kawai a matsayinmu na masu ruwa da tsaki a jam’iyyar domin duba yadda za a ciyar da ita gaba.”