Ba mu ba sulhu da ’yan bindiga — Gwamnatin Katsina
Ƙofarmu a buɗe take domin karɓar duk wani ɗan ta’adda da zai ajiye makamai ya miƙa wuya da zummar rungumar zaman lafiya.
Gwamnatin Katsina ta musanta wasu rahotanni da ke alaƙanta ta da shiga tattaunawar sulhu da ’yan bindiga a jihar.
Da yake zantawa da Aminiya ta wayar tarho, Kwamishinan Labarai da Al’adu na jihar, Dokta Bala Salisu, ya ce har yanzu gwamnatinsu na nan a kan bakarta ta adawa ta duk wata tattaunawar sulhu da ’yan bindiga.
- Kamfanin da ya daina aiki aka ba kwangilar titin Abuja-Kaduna
- NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Kujera Yake Neman Hana Maniyyata Sauke Farali
Sai dai kwamishinan ya ce a kodayaushe ƙofar gwamnatinsu a buɗe take domin karɓar duk wani ɗan ta’adda da zai ajiye makamai ya miƙa wuya da zummar rungumar zaman lafiya.
“Babu mu a duk wata tattaunawar sulhu da ’yan bindiga kuma muna nan akan bakarmu ta karɓar duk wani ɗan ta’adda da zai zubar da makamai ya rungumi zaman lafiya,” inji Dokta Salisu.
Wasu rahotanni a bayan nan na cewa gwamnati ta hau teburin sulhu da wasu ƙasurguman ’yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Batsari da ke Jihar Katsina.
Bayanai sun ce zaman teburin sulhun ya gudana ne tare da wakilan rundunar sojojin Nijeriya da DSS da sarakunan gargajiya da kuma mazauna yankin a ƙauyen Kofa da ke garin Batsari.
Wani mazaunin yankin da ya yi iƙirarin halartar zaman sulhun, ya ce ’yan bindigar sun buƙaci samun aminci wajen shige da fice a cikin ƙauyukan, lamarin da zai kawo ƙarshen hare-haren da suke kai wa.
A kwanakin nan ne wasu daga cikin jagororin ’yan bindigar — Lamu Saudo, Abdulhamid Dan Da, Umar Black da Abu Radda — suka zubar da makamai tare da sakin mutanen da suka yi garkuwa da su.
Wasu majiyoyin soji da suka tabbatar da lamarin sun ce hakan na zuwa ne a sakamakon tsananta ayyukan dakaru a yankin, lamarin da ya sanya ’yan bindigar suka rasa wani zaɓi face rungumar zaman lafiya.