Dokar NCDC: ‘Ba mu ba ’yan majalisa na-goro ba’
Gidauniyar Bill and Melinda Gates ta nisanta kanta daga zargin bayar da toshiyar baki ga ‘yan Majalisar Wakilai don su amince da kudurin nan mai cike da ce-ce-ku-ce na Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC). A ‘yan kwanakin nan dai an zargi gidauniyar da bayar da cin hancin zunzurutun kudin da ya kai har […]
Gidauniyar Bill and Melinda Gates ta nisanta kanta daga zargin bayar da toshiyar baki ga ‘yan Majalisar Wakilai don su amince da kudurin nan mai cike da ce-ce-ku-ce na Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC).
A ‘yan kwanakin nan dai an zargi gidauniyar da bayar da cin hancin zunzurutun kudin da ya kai har dala miliyan 10 ga ‘yan majalisar don su amince da kudurin.
To sai dai a wata wasika da ta aike mai dauke da sa hannun Babbar Daraktarta a Najeriya, Paulin Basinga, gidauniyar ta ce kwata-kwata ba ta da kowacce alaka da zargin da ake yi na bayar da toshiyar bakin.
- Dokar NCDC: Takaddama ta barke tsakanin majalisa da gwamnoni
- Kotu ta tsoma baki a takaddama kan dokar NCDC
A cikin wasikar wacce aka aike wa shugaban kwamitin wucin gadi da Majalisar ta Wakila ta kafa a kan kudurin aka kuma aike da kofin ta zuwa ga Kakakin Majalisa, gidauniyar ta ce zargin da ake mata a wasu daga cikin kafafen yada labaran kasar nan ba su da tushe ballantana makama.
“A zahirin gaskiya, gidauniyarmu ba ta bayar da ko sisin kobo ga Majalisar Wakilan Najeriya ko wata hukuma ta gwamnati don a tabbatar da wannan kuduri a matsayin doka ba.
“Hasali ma, muna iya bakin kokarinmu wajen ganin mun yi taka-tsantsan gami da kiyaye dokokin kowacce kasa”, inji wasikar.
Idan dai za a iya tunawa, bayan ta karbi wani korafi daga Mataimakin Kakakinta, Ahmed Idris Wase, Majalisar ta kafa wani kwamitin bincike a karkashin Henry Nwawuba don gano gaskiyar wannan zargin.
Shi dai kudurin dokar mai cike da ce-ce-ku-ce tuni ya wuce karatu na daya da na biyu a zauren majalisar, ko da yake daga bisani wata kotu ta umarci majalisar da ta dakatar da yunkurin bisa zargin dokar ta yi karan tsaye ga dokokin kasa.
Bugu da kari, kotun ta umarci Kakakin Majalisar Wakilai, Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya da kuma Akawun Majalisar das u bayyana a agabanta a zaman kotun na gaba.