Ba mu ce a kara kudin mai ba – danladi Pasali

Alhaji danladi Garba Pasali shi ne Sakataren kungiyar Dillalan Mai ta kasa, a tattaunawar da ya yi da wakilinmu, ya bayyana dalilan da suka kawo matsanancin karancin man da ake fama da shi a kasar nan. Kuma ya musanta cewa kungiyarsu  ta bukaci gwamnati ta kara kudin mai a Najeriya. Ga yadda tattaunawar ta kasance: […]

Ba mu ce a kara kudin mai ba – danladi Pasali

Alhaji danladi Garba Pasali shi ne Sakataren kungiyar Dillalan Mai ta kasa, a tattaunawar da ya yi da wakilinmu, ya bayyana dalilan da suka kawo matsanancin karancin man da ake fama da shi a kasar nan. Kuma ya musanta cewa kungiyarsu  ta bukaci gwamnati ta kara kudin mai a Najeriya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

Me ya kawo matsanancin karancin man fetur da ake fama da shi a kasar nan, bayan ka yi bayani a kwanakin baya, cewa za a shawo kan matsalar?

Wato an samu matsala ce, domin matatun mai guda 4 da ake da su a kasar nan a Kaduna da Warri da Fatakwal, man da suke tacewa ba ya wadata kasar nan. Kuma kasancewar mun shiga yanayin karshen shekara, musamman a wannan lokaci na bikin Kirsimeti inda za a ga mutane suna ta tafiye-tafiye. Don haka duk lokacin da irin wannan lokaci ya zo ana samun irin wannan matsala. Domin kafin wannan lokaci ana amfani da litar mai miliyan 28 zuwa miliyan 30, amma yanzu a wannan lokaci ana amfani da lita miliyan 45 zuwa miliyan 50.  Kuma ga jita-jitar da aka yi ta yadawa cewa za a kara kudin mai a kasar nan, kuma wadansu suna cewa idan aka shiga sabuwar shekara za a shiga matsalar mai. Wannan ne ya sanya mutane suka tsorata suka yi ta sayen mai suna boyewa. 

Za ka ga mutumin da a da yake sayen mai na Naira dubu 1 ko dubu 2 yanzu ya zo yana sayen mai na Naira dubu 5 ko dubu 10 ya boye. Wannan yana cikin abubuwan da suka kawo wannan matsala ta karancin mai a kasar nan.

Sannan akwai yanayi na hutu a kasashen duniya, Turawa suna rufe matatun man kasashensu suna tafiya hutu. Wannan shi ma yana daga cikin abin da ya kawo karancin man. Saboda a yanzu hutun da aka tafi ya sanya tashin mai a duniya, wannan tashin man ya shafi Najeriya, domin kashi 60 na man da muke amfani da shi a kasar nan, ana shigo da shi ne daga kasashen waje. 

Don haka ’yan kasuwar da suke sayo mai daga kasashen waje kusan kashi 90, sun bar wa Kamfanin Mai na kasa (NNPC) ne aikin shigo da shi. Duk inda aka samu yanayi irin wannan ana samun matsalar karancin mai. 

Ana zargin cewa ku dillalan mai saboda boye wannan mai ne da kuke yi, ya sanya ake samun wannan matsala ta karancin mai a Najeriya, me za ka ce?

Wannan magana gaskiya ce domin ka san duk inda aka samu mutane da yawa dole ne a samu irin wannan. Domin ka ga kamar a wannan kungiya muna da mutane masu gidajen mai sama da dubu 50, don haka duk inda aka samu yawan jama’a haka dole ne a samu bata-gari. Don haka ba za mu ce, ba za a samu irin wadannan masu boye mai a cikin mutanenmu ba. Akwai bata-gari a cikin kungiyarmu kuma akwai wadanda suke sanya rigarmu, domin su ba ’ya’yan wannan kungiya ba ne. Duk gidajen man da kake gani a kasar nan, ba kowanne ne yake da lasin ba, kuma ba kowanne ne dan kungiyarmu ba. 

Don haka muke kira ga Hukumar Kula da Gidajen Mai (DPR) da mu kanmu a matsayinmu na kungiyar Dillalan Mai ta Najeriya mu kafa kwamiti na musamman mai sanya ido tare da lura da wadanda ake bai wa mai a kasar nan da wuraren da suke kai man. 

Mun samu matsala a tsakaninmu da Kamfanin NNPC, domin a Kamfanin NNPC akwai wurin da ake zama a kula da su wane ne ake bai wa mai kuma ina ne suke kai man. Abin mamaki shi ne a wannan karo ba su sa kungiyar Dillalan Mai a cikin wannan aiki ba. Kai ne ka san matsalar gidanka kuma kai ne ka san yadda za ka magance matsalar gidanka, ba wani da yake waje ne, zai zo ya fi ka sanin matsalarka ba.

Kamar yadda aka yi a lokacin da aka samu irin wannan matsala a shekarar 2015. Mu kungiyar Dillalan Mai ne muka kawo hanyar da aka bi aka magance wannan matsala ta karancin mai a kasar nan. Saboda dan man da aka samu, muna duba mutanen da suka cancanta suka san ya kamata, wajen ganin su ne aka ba su man. 

Idan muka ba mutum mai za mu bi shi har zuwa gidan mansa, mu tabbatar cewa ya sauke wannan mai a gidan man, kuma ya sayar wa mutane a kan farashin gwamnati.  

To, a wannan karon sai Kamfanin NNPC ya dauka shi kadai zai yi wannan aiki, wannan abu da suka yi yana daga cikin abin da ya kawo wannan matsala ta mai a Najeriya, shi ya sa idan aka raba mai, sai a rasa inda yake shiga. 

A ‘yan kwanakin nan an ji labarin cewa kungiyarku ta bukaci gwamnati ta kara kudin mai, mene ne dalilinku na wannan bukata?

Mu dai a yanzu gaskiyar magana ba ma neman a kara kudin mai a Najeriya. Abin da muka ce wa gwamnati shi ne Mataimakin Shugaban kasa yana maganar cewa ya kamata mu ma mu taimaka mu je mu sayo mai daga waje. Mun gaya musu cewa gaskiyar magana wannan mai idan aka sayo shi daga waje lita daya tana kaiwa Naira 171. Ka ga ita kuma gwamnati ta ce ba za ta kara kudin mai ba. To ka ga mu ’yan kasuwa ba zai yiwu mu je mu sayo mai a kan lita naira 171 kuma mu zo mu sayar da lita Naira 145 ba. Wannan aiki gwamnati ce kadai za ta iya yi, don haka ba mu ce gwamnati ta kara kudin mai ba. Mu ma ba ma goyon bayan kara kudin mai a Najeriya, amma dole ne gwamnati ta duba yadda za ta warware wannan matsala, kan sanya tallafi kan wannan alamari domin idan babu tallafi babu yadda za a yi mu je mu sayo mai kan lita Naira 171, mu zo mu sayar da lita a Naira 145. Wannan ita ce matsalar da muka nuna wa gwamnatin, amma ba maganar a kara kudin mai ba. Babu wanda yake son a kara kudin mai a Najeriya. 

Mu kanmu kara kudin mai yana yi mana illa domin yana rage mana karfin jari. Saboda misali idan jarinka zai iya ba ka mota uku, idan aka kara kudin mai jarinka zai dawo mota biyu ne. 

A baya an yi bayanin cewa idan gwamnati ta cire tallafin mai za a warware matsalar karancin mai a Najeriya. Sai ga shi bayan da gwamnatin ta cire tallafin har yanzu ana fama da matsalar me ya kawo haka?

Gwamnati ba ta janye hannunta ba. Ai Kamfanin Mai na kasa (NNPC) na gwamnati ne kuma kashi 90 cikin 100 na man da ake shigowa da shi daga waje Kamfanin NNPC ne yake shigowa da shi. Ka ga wannan ya nuna cewa har yanzu gwamnati ce take yin komai kan harkar mai a Najeriya. Da gwamnati ta karfafa’yan kasuwa ta ba su dama za a samu gasa, idan aka samu gasa a tsakanin ’yan kasuwa, farashin man zai sauka, abin da muke fada ke nan. Idan aka bar ’yan kasuwa suka shigo da kaya dole ne kaya ya fadi. Ko a kasuwa idan aka kai kaya da yawa kaya yana faduwa, amma idan kaya ya yi karanci dole ne farashin kayan ya tashi. 

To yanzu halin da ake ciki gwamnati ce take kawo mai daga waje da kashi 90 cikin 100. Idan da gwamnati za ta bar ’yan kasuwa su rika shigo da mai duk inda mai yake a duniya za su je su sayo. Ai akwai kasashen da babu ruwansu da irin wannan yanayi na hutun karshen shekara. Idan ka tafi kasashen Asiya kamar Rasha da China za ka je ka kawo kayanka, domin su ba su san wani Kirsimeti ko karshen shekara ba.