Ba mu da hannu a kama Sowore — DSS
Hukumar ta nesanta kanta daga kama Sowore da safiyar ranar Lahadi.
Hukumar Tsaro ta DSS ta ce jami’anta ba su da hannu a kama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, a zaɓen 2023.
DSS, ta bayyana haka ne a matsayin martani ga rahotannin da ke yawo a kafafen yaɗa labarai cewa jami’anta ne suka kama shi.
- Farashin kwandon tumatir ya faɗi daga N10,000 zuwa N1,000 a Gombe
- Yadda Masarautar Kaltungo ke yakar yunwa da fatara — Mai Kaltungo
Wani babban jami’in DSS ya shaida wa Aminiya cewa ba su da hannu a kamen.
Rahotanni sun nuna cewa an kama Sowore ne da safiyar ranar Lahadi a filin jirgin na Murtala Muhammad da ke Lagos.
An ruwaito cewar hukumar jami’an shige da fice na ƙasa ne suka kama shi, amma daga bisani sun sake shi.
Sowore, ya dawo Najeriya daga Amurka ne, amma ya fe an karɓe fasfo ɗinsa, kuma an sanar da shi cewar umarni aka bayar na kama shi.
Sai dai, bayan sa’o’i kaɗan, ya wallafa a shafinsa na X cewar an sake shi, kuma an dawo masa da fasfo ɗinsa.
Wani babban jami’in DSS, ya bayyana cewa sun cire sunan Sowore daga jerin sunayen waɗanda suka sanya wa ido a baya.
Ya kuma ce sabon Daraktan DSS yana ƙoƙarin yin gyara a hukumar don inganta ayyukanta.
DSS, ta jaddada cewa jami’anta ba su da hannu a kama Sowore, kuma ta buƙaci ‘yan Najeriya su yi watsi da wannan labarin.
Sai dai har yanzu babu cikakken bayani daga DSS, kan lamarin.