Ba mu da hannu a samamen da aka kai hedikwatar NLC — DSS

Lamarin ya faru ne yayin da ake ci gaba da zanga-zangar tsadar rayuwa.

Ba mu da hannu a samamen da aka kai hedikwatar NLC — DSS

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS ta ce babu hannunta a samamen da aka kai wa hedikwatar Kungiyar Kwadago ta NLC.

Aminiya ta ruwaito cewa a jiya Laraba da daddare ne dai wasu jami’an tsaro ɗauke da manyan makamai da fuskoki rufe suka kai samame ofishin ƙungiyar, tare da yin awon gaba da wasu takardu.

Lamarin dai ya faru a daidai lokacin da ’yan Nijeriya suke ci gaba da gudanar da zanga-zangar kwana 10 kan neman a kawo ƙarshen tsadar rayuwa a ƙasar, inda a yau aka shiga kwana ta kakwas.

Ƙungiyar ta NLC ta zargi jami’an tsaron farin kaya na DSS ta ƙaddamnar da samamen.

Kungiyar ta ce jami’an sun yi dirar-mikiya a ginin hedikwatar ta ne da ake kira Labour House, tun da daddare da misalin karfe 8:30.

“A ranar Laraba da misalin karfe 8:30 na dare gomman jami’an tsaro ɗauke da makamai sun kai wa ginin Labour House hari,” a cewar wata sanarwa da NLC ta fitar a safiyar Alhamis.

Sai dai a zantawarsa da Aminiya, mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya ya musanta zargin.

“’Muna so kowa ya sani cewa jami’an DSS ba su kai kowane irin samame kan ofishin NLC da ke Abuja ba”, in ji Afunanya.

A ƙofar banɗakin Gidan Yarin Kuje nake kwana — Ɗan zanga-zanga

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7