Ba mu da kyakkyawar alaka da gwamnati – ’Yan Kasuwar Sansanin Alhazai
Kungiyar ‘Yan kasuwar sansanin alhazai da aka fi sani da Hajj Camp da ke Kano sun koka game da rashin samun kyakkyawar alaka tsakaninsu da gwamnati, Shugaban kungiyar Alhaji Nazir Abdullahi Sule ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Aminiya. Shugaban ya bayyana cewa gwamnati ba ta bai wa kungiyarsu muhimmanci domin […]
Kungiyar ‘Yan kasuwar sansanin alhazai da aka fi sani da Hajj Camp da ke Kano sun koka game da rashin samun kyakkyawar alaka tsakaninsu da gwamnati, Shugaban kungiyar Alhaji Nazir Abdullahi Sule ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Aminiya. Shugaban ya bayyana cewa gwamnati ba ta bai wa kungiyarsu muhimmanci domin duk abin da gwamnati za ta yi a kasuwar ba ta tuntubar kungiya haka kuma idan tana neman wasu bayanai ba ta nema daga kungiya sai dai wasu da ke gefe da ke sanar da ita bayanan da ba na gaskiya ba.
Alhaji Nazir ya kara da cewa, baya ga haka babbar matsalar da kasuwar ke fuskanta ita ce ta rashin wadatattun shaguna a kasuwar, inda mafi yawancin ‘yan kasuwar ke gudanar da kasuwancinsu a gefen hanya ba tare da samun wurin da za su kasa hajarsu ba.
“Mun kai korafinmu ga gwamanti ya fi sau shurin masaki a kan muna bukatar a gina mana shaguna a kasuwarmu kasancewar muna da fili wanda kuma mallakin gwamnati ne, amma har yanzu ba a yi mana ba. hakan ya jawo wa ’yan kasuwarmu bin gefen hanya suna kasa kayayyakinsu” Alhaji ya bayyana cewa ‘yan kasuwar ba su amfana da ire-iren shagunan
da gwmanatin ta gina a lokutan baya ba kasancewar a maimakon da gwamnatin ta gina shagunan ta raba su ga ‘yan kasuwa sai ta damka a hannun wasu mutane da ba ‘yan kasuwar ba, inda suka bayar da shagunan ga ‘yan kasuwar da tsada.
“Abin takaicin shi ne a lokacin da gwamnati ta gina wasu shaguna yan kasuwar wadanda su suka raya wurin shekara da shekaru suna kasuwanci a wannan waje ba su sami komai ba, sakamakon gwamnati ta damka shagunan ga wasu na kusa da ita wadanda ba ‘yan kasuwar ne na hakika ba inda su kuma suka bayar da su haya ga ‘yan kasuwar bisa kudi masu yawa. Kin ga hakan ba a kyauta wa ‘yan kasuwa ba kasancear su suka raya wurin tun yana daji har ya rayu. Hakan ya jawo irin wadannan ‘yan kasuwar suka samu matsala ta cuta yayin da wasu kuma suka hadu da karayar arziki domin ana tashe su a inda suke neman abinci ba tare da sama musu wani wurin ba. Da a ce gwamnati ta hada kai da kungiya to na tabbata yan kasuwa za su sami shagunan kamar yadda ya dace.”
A cewar Shugaban kasuwar tana fuskantar matsalar rashin fitilar hanya, wanda ya ce hakan ba karamin cikas yake haifarwa a kasuwar da kuma masaukin alhazai ba “yawanci mukan kai har karfe tara zuwa goma na dare, sai dai saboda rashin fitilar titi sai gashi har an fara yi mana sace-sace tare da kwace, Ba don Allah ya sa mun dauki mataki ta hanyar hadin kai da ‘yan sanda inda aka kama ire-iren barayin to da Allah ne kadai ya san inda abin zai tsaya. Haka kuma idan lokacin aikin hajji ya zo ‘yan kasuwarmu har kwana suke yi anan wajen hada-hadar kasuwanci tare da alhazai. Kin sana wasu alhazan bas u zuwa da jakarsu kuma ba su so su isa ga iyalinsu ba tare da sun rike wani abu na tsaraba ba kamar zamzam da dabino da ‘yar alawa don yara. Kai
ina ganin ko ba don mu ‘yan kasuwa ba, harkar jigilar alhazai kadai ta isa gwamnati ta sanya fitilar kan titi a wannan hanya, Kowa ya san cewa a wasu lokutan akan kira alhazan da za su tashi cikin dare ko kuma jirgi ya sauke su cikin dare, to idan aka ce ba haske a wurin kin ga akwai hadari a wannan lamari” Shugaban ya musanta zargin da ake yi wa ‘yan kasuwar cewa akan hada baki da su wajen batar da kayan alhazai, inda ya ce ‘yan kasuwarsu suna yin uwa da makarbiya a sha’nin tashi da saukar alhazai inda kungiya take taimaka wa da jami’an tsaronta wajen yin wannan aiki baya ga daidaikun mutane da ke taimakawa harkar don neman lada a wurin Allah. “kamar lokaci irin wanann mukan yi kokari wajen ganin an gudanar da aikin jigilar alhazai lami lafiya.
Baya ga mutanenmu da ke yi wa alhazai hidima da kudin aljihunsu akwai masu ba su ruwan sha da abinci kyauta don neman lada a wurin Allah. Haka kuma kungiya tana tura jami’an tsaronta kamar mutum 10 don bayar da gudummowa wajen ganin an tsare dukiyar alhazan nan. Wallahi ni da kaina ina zuwa cikin wurin a gudanar da wannan aiki tare da ni.
A wani lokaci sai na kai karfe biyun dare ana gudanar da aikin alhazai . Kin ga batun ma a ce ana samun wasu daga cikin ‘yan kasuwarmu da hannu cikin batan kayan alhazai bai ma taso ba, domin duk mun toshe kafar yin hakan”
Alhaji Nazir ya yi kira ga alhazai da su daina sayo kayan tsaraba daga kasa mai tsarki kasancewar kasuwarsu an kafa ta ne don taimaka wa alhazai kama daga kan abincin da za su ci da kuma kayayyakin tsaraba, don haka sun tanadar wa alhazai daukacin kayayaykin da suke bukata don tsaraba.
”kasuwarmu wata karamar Makka ce domin duk wani abu da ake samu a kasar Saudiyya, musamamn wanda ake tsaraba da shi to muna sayar da shi, kama daga kan dabino da Zamzam da darduma da bagaruwa da Jallabiya da sauransu. Bambancin da ke tsakanin kayanmu da na Saudiyya bai fi tazarar Naira dari zuwa dari biyu ba. wanda kuma idan mutum ya auna wahalar da yake sha wajen dauko kayan wanda a wasu lokutan suke zame musu matsala ba. Muna kokari wajen tabbatar da cewa kayayyakin da ake sayarwa a kasuwarmu an sayar da su cikin sauki, kuma masu inganci domin a irin wanann lokaci mukan kafa kwamiti da ke yawo a kasuwa don gano mana kaya marasa kyau a kasuwar, wanda idan mun samu mukan kwace tare da hukunta mai kayan”.