Ba mu da niyyar amfani da malaman jami’a don magudin zabe – Bafarawa

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato kuma daya daga cikin dattawan Jam’iyyar PDP a jihar, Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa ya musanta zargin da Gwamnan Jihar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi cewa shi da Mai Ba Shugaban kasa shawara kan Harkokin Tsaro, Kanar Sambo Dasuki sun yi taro da malaman jami’oi don amfani da su wajen magudin […]

Ba mu da niyyar amfani da malaman jami’a don magudin zabe – Bafarawa
Ba mu da niyyar amfani da malaman jami’a don magudin zabe – Bafarawa

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato kuma daya daga cikin dattawan Jam’iyyar PDP a jihar, Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa ya musanta zargin da Gwamnan Jihar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi cewa shi da Mai Ba Shugaban kasa shawara kan Harkokin Tsaro, Kanar Sambo Dasuki sun yi taro da malaman jami’oi don amfani da su wajen magudin zaben Shugaban kasa a jihohin Sakkwaton da Kebbi da Zamfara.

Kakakin tsohon Gwamnan, Malam Yusuf Dingyadi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Sakkwato, inda ya ce Bafarawa ya bayyana wannan zargin da zama abin dariya, kuma shirme domin cin zarafin malaman jami’o’i.
Alhaji Bafarawa ya ce, ba dalilin da zai sa sai Jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato ta bi wata hanya da magudin zabe kafin ta lashe kuri’a a zaben Shugaban kasa na ranar 28 ga Maris, domin a yanzu ba shakka, Sakkwato da Kebbi da Zamfara jihohin PDP ne saboda karbuwar da Shugaba Goodluck Jonathan ya samu.
“Ayyukan alheri na raya kasa da ci gaban al’umma da Shugaba Jonathan ya samar wa al’umarmu da kuma dimbin fatan alheri da muke samu dare da rana daga jama’a sun tabbatar da cewa da iznin
Allah za mu lashe zabe a wadanan jihohi,” inji Bafarawa.
Tsohon Gwamna Bafarawa, ya nuna bacin ransa kan yadda wasu masu rike da mukaman siyasa ke amfani da mukamansu domin cin mutunci da zarafin wasu jama’a domin cimma buri na siyasa. Ya ce malaman jami’o’i wadanda suke ta fadi-tashin ilimantar da yara da cusa musu tarbiyya, sanya su cikin lamarin siyasa domin biyan wata bukata abin takaici ne da zai yi illa ga ci gaban siyasa da dorewar dimokuradiyya.
Ya ce, a lokacin da Sambo Dasuki ya je Sakkwato domin ziyarar ’yan uwa da sada zumunci, shi Bafarawa yana kasar waje, don haka ta yaya zai iya gudanar da taro da malaman jami’o’i?