Ba mu da Ofishin Matar Gwamna a Jihar Kebbi – Uwargidan Gwamna

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya A’isha Atiku Bagudu kuma Shugabar Gidauniyar Tallafa wa Mata da Almajirai da Marayu (MALLPAI) ta nuna rashin jin dadinta kan yadda wasu kafafen watsa labarai ke shiga hakkinsu, inda suke yayata batun iyalan Gwamnan Jihar, Alhaji Atiku Bagudu ba tare da bin ka’idar aiki ba.Uwargidan ta bayyana haka ne a […]

Ba mu da Ofishin Matar Gwamna a Jihar Kebbi – Uwargidan Gwamna
Ba mu da Ofishin Matar Gwamna a Jihar Kebbi – Uwargidan Gwamna

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya A’isha Atiku Bagudu kuma Shugabar Gidauniyar Tallafa wa Mata da Almajirai da Marayu (MALLPAI) ta nuna rashin jin dadinta kan yadda wasu kafafen watsa labarai ke shiga hakkinsu, inda suke yayata batun iyalan Gwamnan Jihar, Alhaji Atiku Bagudu ba tare da bin ka’idar aiki ba.
Uwargidan ta bayyana haka ne a yayin tattaunawa da wakilinmu a Abuja, inda ta ce tun da farkon hawan mijinsu gadon mulki, ya sanar da duniya cewa ba zai tafiyar da tsarin Ofishin Matar Gwamna (First Lady) ba a gwamnatinsa.
Uwargidan Gwamnan wadda ta amsa tambayar ko gidauniyarta tana da nasaba da batun ofishin Matar Gwamna, ta ce: “Ya kamata in sanar da al’umma cewa, wannan gidauniya mun fara ta ne tun a shekarar 2009, kafin maigidana ya fara harkokin siyasa, wato tun kafin ya zama Sanata, balle daga bisani ya zama Gwamna. Shin bari ma in tambaye ka, mene ma’anar First Lady? Maigidanmu ya shaida mana cewa shi a Jihar Kebbi ba ya da First Lady, babu ruwansa da First Lady, yana dai da matansa na aure a matsayinsa na Gwamna. Ya fada, ya kira ku ’yan jarida, an buga a jaridu an fada a talabijin da rediyo. Ban san me ya sa ku ’yan jarida kuke ta yayata maganar First Lady, First Lady ba. Yadda ka ce, kwarai kuwa ni ce uwargidansa, domin ni ce matarsa ta farko. Kuma idan ma ta wannan kuke, shi kansa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ai ya ce babu wannan ofishi na First Lady a gwamnatinsa, to tunda mu ma maigidanmu a matsayinsa na Gwamna ya ce ga abin da yake so, saboda me ba za a martaba matakin da ya dauka ba? Bai kamata ku ’yan jarida ku rika daukar cewa waccan ko wannan ce First Lady ba, ana daukar labarai na tashin hankali da hada fitina a cikin gida. Ku ya kamata ku taimaka, wadannan maganganun su mutu, tunda mutum ya ce ga abin da yake so, to a yi masa haka mana.”
Game da yadda gidauniyarta ta MALLPAI ke samun kudin aiwatar da ayyukan tallafa wa al’umma kuwa, Hajiya A’isha ta ce: “Mu mukarraban gidauniyar ne muke fitar da dukiyarmu kuma al’umma da kungiyoyin gama-kai masu zaman kansu suna tallafa wa ayyukanmu. Haka shi ma maigidana, Gwamnan Jihar Kebbi yana tallafa mana da dukiyarsa da kuma shawarwari. Ya ma yi alkawarin ci gaba da ba mu irin wannan tallafi, don haka muna yi masa godiya da addu’ar Allah Ya biya shi.”