Ba mu da shirin kara farashin man fetur a kwanan nan – NNPCL

Kamfanin ya ce har farashin zai ci gaba da zama yadda yake

Ba mu da shirin kara farashin man fetur a kwanan nan – NNPCL

NNPCL

Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL) ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa yana shirye-shiryen kara farashin man fetur a kwanan nan.

Kamfanin ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a dandalinsa na X (Twitter a da) ranar Juma’a.

Ya ce, “Sabanin jita-jitar da ake ta yadawa, ba mu da shirin kara farashin man fetur.”

NNPCL ya ce har yanzu gidajensa na ci gaba da sayar da man a kan farashi mai rahusa.

A cewar kamfanin, “Ya ku abokan huldarmu, mu a gidajen man NNPC muna alfahari da cinikinku, sannan ba mu da shirin sake kara farashin man sabanin yadda ake ta yadawa. Ku yi kokari ku ci gaba da sayen ingantaccen mai a gidajenmu da ke fadin kasar nan a farashi mai rahusa.

Tun bayan cire tallafin mai a karshen watan mayun da ya gabata dai, NNPCL ya kara farashin mai akalla sau biyu.

Sai dai tun a farkon makon nan ne dai aka ga galibin gidajen man ’yan kasuwa sun kasance a rufe, sai ’yan tsirari da suke sayarwa a kan farashi mai tsada, yayin da ake fargabar yin karin kudin.