Ba mu da shirin sake bude makarantu yanzu – Gwamnatin Kano
Gwamnatin jihar Kano ta musanta rahotannin da ke cewa tana kokarin sake bude makarantu a jihar. Wasu rahotanni dai sun yi ta yawo a ‘yan kwanakin nan cewar gwamnatin jihar ta kafa kwamiti don duba yiwuwar sake bude makarantu bayan da annobar coronavirus ta tilasta rufe su tun da farko. To sai dai a wata […]
Gwamnatin jihar Kano ta musanta rahotannin da ke cewa tana kokarin sake bude makarantu a jihar.
Wasu rahotanni dai sun yi ta yawo a ‘yan kwanakin nan cewar gwamnatin jihar ta kafa kwamiti don duba yiwuwar sake bude makarantu bayan da annobar coronavirus ta tilasta rufe su tun da farko.
To sai dai a wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta jihar ta fitar ta bakin kakakinta, Malam Yusuf Aliyu ta bayyana labarin a matsayin na kanzon kurege.
Ya ce labarin ba shi da tushe ballantana makama.
Sanarwar ta kuma ce, “Jihar Kano, kamar sauran jihohi ta karbi wata takarda daga Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya kunshe da matakan da za a bi kafin sake bude makarantu a lokacin da ya dace, inda aka umarce mu da mu yi nazari kuma mu bayar da tamu shawarar.
“A kan haka ne ma’aikatar ilimi ta kafa wani kwamitin wucin-gadi don yin nazarin, kuma duk abind suka bayar da shawara za a mayar wa da ma’aikatar ilimi ta tarayya”, inji sanarwar.
‘Ba mu hana koyarwa ta intanet ba’
Kazalika gwamnatin ta musanta labarin cewa ta dakatar da makarantu masu zaman kansu daga koyar da dalibansu ta hanyar fasahar sadarwa ta zamani.
“Shi ma wannan labarin babu kanshin gaskiya a ciki domin tuni ita ma gwamnati ta dukufa wajen koyar da dalibanta ta gidajen rediyo da talbijin da ke jihar”, inji Yusuf.
Ya ce abin da gwamnati ta haramta wa makarantun shi ne shirya jarrabawa ta fasahar tunda dai gwamnati ta riga ta dakatar da zangon karatu na biyu a tsarin kalandar karatu ta bana.
“Mun rarraba wasikun gargadi ga makarantu kan kada su kuskura su shirya wa dalibai jarrabawa a halin da ake ciki.
‘Yadda makarantu ke karya dokar’
“Sai dai majiya mai tushe ta shaida mana cewa wasu makarantun sun yi kunnen uwar shegu da umarnin.
“Wasu makarantun ma labari ya iske mu sun bige da koya darussa ta fasahar har jarabawa suke shirya wa daliban.
“Wasu kuma suna karbar kudade masu yawa daga iyayen yara da sunan kudin darussan da kuma kudin damar shiga yanar gizo. Kai wasu ma har sun fara karbar kudin makaranta na zangon karatu na uku”, inji sanarwar.
‘Makarantun da suka karya dokar za su yaba wa aya zakinta’.
Za a hukunta masa sabawa
Gwamnatin ta ce za ta hukunta wadanda duk suke da hannu wajen karya dokar.
“Wannan yin karan tsaye ne ga dokar da gwamnatin Kano ta shimfida.
“Tuni ma’aikatar ilimi ta tattara bayanai da hujjoji kan wadanda suka karya wannan dokar ta gwamnati kuma nan ba da jimawa ba za mu gayyaci masu wadannan makarantun don su girbi abin da su ka shuka”, inji Yusuf.
Ko a makon da muke ciki dai sai da Gwamnatin Tarayya ta bakin Kwamitin da ta kafa na Kar-ta-kwana don yaki da annobar coronavirus ta gargadi gwamnatocin jihohi kan sake bude makarantun.