Ba mu da shirin sake kara farashin man fetur a yanzu – Tinubu
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da IPMAN ke cewa man zai iya tashi
Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya ba ’yan Najeriya tabbacin cewa gwamnati ba ta da shirin sake kara farashin man fetur a yanzu haka.
A kwanan nan ne dai jami’in hulda da jama’a na Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN), Chinedu Okadike, ya bukaci ’yan Najeriya da su shirya fuskantar karin farashin man saboda faduwar darajar Naira.
- Kenya ta dawo da tallafin mai bayan fuskantar matsin lambar jama’a
- Faccala ta lakada wa faccalarta duka da itace a Kano
To sai dai da yake magana ta bakin mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, Shugaba Tinubu a cikin wata sanarwa ranar Talata ya ce ’yan Najeriya su sha kuruminsu ba za a kara farashin ba a nan kusa.
Ya ce, “A yau da safen nan, na sami damar zama da Shugaba Tinubu, inda muka tattauna a kan halin da ake ciki kan batun samar da man fetur.
“Yana ba ’yan Najeriya tabbacin cewa dukkan masu ruwa da tsaki na na suna nazari a kan batun. Sannan akwai ma barazanar da kungiyoyin kwadago suka yi idan aka kara farashin.
“Bayan haka kuma, Shugaban yana tabbatar wa jama’a cewa kari a kan sanarwar da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya yi jiya cewa babu batun karin a yanzu a kowanne sashe na kasar nan.
“Muna kara jaddadawa, babu batun kara farashi a kowanne bangare na Najeriya a halin da ake ciki,” in ji Kakakin Tinubu.