“Ba mu da wata alama da take bambanta mu da juna”
Aminiya ta samu ganawa da wasu tagwaye Hassan da Hussaini masu sana’ar dinki a Jihar Legas wadanda saboda tsananin kamanin da suka yi da juna abokanen huldarsu ba sa iya tantace su. Tagwayen sun bayyana cewa hatta iyayensu ba sa iya tantance su har sai sun yi musu bayani: Za mu so ku gabatar da […]
Aminiya ta samu ganawa da wasu tagwaye Hassan da Hussaini masu sana’ar dinki a Jihar Legas wadanda saboda tsananin kamanin da suka yi da juna abokanen huldarsu ba sa iya tantace su. Tagwayen sun bayyana cewa hatta iyayensu ba sa iya tantance su har sai sun yi musu bayani:
Za mu so ku gabatar da kanku?
Sunanmu Hassan da Hussaini. Sunan mahaifinmu Malam Abdulkadir, shekarunmu sun kai kimanin 23 a duniya. An haife mu a unguwar dandago da ke cikin birnin Kano. Mun yi makarantar firamare a can Kano bayan mun kammala da mahaifinmu ya rasu sai aka dawo da mu Legas domin mu ci gaba da karatu da gudanar da rayuwa kamar yadda muka saba.
Me ye dalilin da ya sa aka dawo da ku Jihar Legas?
Bayan mahaifinmu ya rasu sai wani kanin mahaifiyarmu ya dawo da mu jihar Legas don mu ci gaba da karatun sakandire bayan mun kammala muna shirye-shiryen tafiya makaranta ta gaba don ci gaba da karatu amma mun koyi sana’ar dinki a yanzu ita muke yi muke rufa wa kanmu asiri.
Mutane da dama suna cewa kun yi kama da juna ta yadda ba su iya bambance ku, shin kun san kun yi kama da juna?
Gaskiya mu kanmu mun san mun yi kama da juna kwarai da gaske don idan ka kalle mu za ka ga komai namu daya ne tun daga fuska har zuwa tafin kafa, sai ka yi da gaske sannan za ka iya bambance mu. Muryarmu daya, tsawonmu daya, kamaninmu daya komai namu daya, wuri daya muke kwana, tare muke yawo ba ma rabuwa da juna, kai hatta kudi tare muke kashe kudinmu ba ma warewa.
Shin har ’yan uwanku da iyayenku ba sa iya tantance ku?
Gskiya ne, ita kanta mahaifiyarmu ba ta iya gane mu wani lokaci za ta kira Hassan da sunan Hssaini ko ta kira Hussaini da sunan Hassan, sai mun yi mata bayani sannan ta gane. Su kuwa ’yan uwanmu kodayaushe ba su iya gane mu. Ko mai gidanmu da sauran mutanen da muke aiki a shago daya ba su iya gane mu duk da cewa kodayaushe muna tare a wurin sana’a. Komai tare muke.
Su ma mutanen gari da sauran abokanen huldarku suna cewa ba sa iya gane ku, shin gaskiya ne?
kwarai da gaske, mun ce maka hatta mahaifiyarmu da ta haife mu ba ta iya bambance mu balantana sauran jama’ar gari. Wani lokaci idan aka ba Hussaini aiki sai ka ga idan mai karba ya zo sai ya nufi wurin Hassan ya rika tambayarsa aikin da ya ba shi. Wani lokaci kuma idan aka ba Hussaini aiki sai a zo wurin Hassan a rika tambayarsa aikin. Kai idan wani ya yi wata hulda da Hassan sai ya tare ni a wani wuri ya rika tambayata huldar da suka yi da Hussaini, sai na yi masa bayani dalla-dalla sannan ya gamsu. Wani lokaci ma wasu ko da mun yi musu bayani ba su yarda sai su ga kamar shirya musu karya muka yi.
Shin akwai alama da za a iya tantance ku da ita?
Gaskiya babu wata alama da mutane za su yi amfani da ita wajen tantance mu. Saboda komai namu daya ne da murya da kalar fata da tsawo da tafiya da kuma dabi’a. Saboda haka sai dai mutane su ci gaba da kirdado har su gano alamun da za su rika gane mu.
Shin wane al’amari ne da ya faru da ku da ba za ku taba mantawa ba sakamakon kamannin da kuka yi da juna?
Gaskiya ba za mu manta da abubuwa da dama da suka auku ba. Kamar ni Hassan, ba na mantawa da wata rana ina tafiya sai wani mutum ya tare ni yana tambayata dinkin da ya ba dan uwana, sai da na yi masa bayanin cewa ba ni ya ba dinki ba sannan daga bisani ya gane ba wanda ya ba dinki ba ne. Irin haka ta yi ta faruwa da mu da yawa. Wani lokaci ma idan wani daga cikinmu yana tafiya sai a tare shi a rika yi masa wasu maganganun da bai san su ba. Ko kuma idan muna tafiya tare sai a tsayar da mu a rika mamakin kamannin da muka yi da juna.
Shin kukan samu sabani a tsakaninku?
Muna samun sabani da bacin rai a tsakani. Ka san ko da harshe da hakori suna samun sabani balantana tsakanin mutum da mutum amma idan muka samu sabani da kanmu muke sasanta junanmu ba tare da mun bar wani ya shigo tsakaninmu ba.
Ga shi yanzu kuna yin komai tare, shin kuna da burin idan kuka tashi yin aure ku auri tagwaye?
Muna da burin idan muka tashi yin aure mu auri tagwaye irinmu ba tare da wani bambanci ba. Gaskiya idan muka samu haka za mu ji dadi a rayuwarmu. Don gaskiya muna so mu ci gaba da rayuwa tare ba ma son mu rabu da juna kuma ba ma son mu yi nesa da juna.
To yanzu idan daya daga cikinku ya samu canjin sana’a yaya za ku yi?
Idan Allah ya sa daya daga cikinmu ya samu canjin sana’a babu yadda za mu yi, ka san kowa da inda Allah Ya sanya abincinsa da arzikinsa, Idan ubangiji Ya sanya wani daga cikinmu yana da abinci a wata sana’a, babu yadda za mu yi sai mu zura wa sarautar Allah ido. Idan kuma Allah Ya sanya sana’a daya za mu ci gaba da yi har zuwa karshen rayuwarmu to haka muke so.